in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta tsaurara matakan tsaro gabanin zaben shugaban kasa
2019-02-14 09:58:35 cri
Hukumomi a Najeriya sun bada umarnin a tsaurara tsaro a duk fadin kasar a yayin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasar a ranar Asabar mai zuwa.

Hukumar 'yan sandan kasar ta ce domin a samu nasarar gudanar da zabukan cikin kwanciyar hankali, hukumar ta riga ta tura jami'anta kuma za ta yi amfani da dukkan jami'anta da kayan aikin da take da su don samun nasarar zabukan.

Kakakin hukumar 'yan sandan kasar Frank Mba, ya fadawa 'yan jaridu a Abuja cewa za'a tura jami'an a dukkan sassan kasar domin samar da cikakken tsaro da kwanciyar hankali.

A cewar Mba, 'yan sandan dake tsaron teku da masu kula da harkar sararin sama sun shirya tsaf domin tabbatar da ganin an gudanar da zaben cikin nasara. Ya ce an tanadi jiragen sama masu saukar ungulu wadanda za'a yi amfani da su wajen kai daukin gaggawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Dukkan bangarorin tsaro da musamman na hukumar 'yan sandan kasar sun kammala duk wasu shirye-shirye domin tunkarar zabukan.

Mba ya ce, 'yan sanda da sauran hukumomin tsaron kasar sun shirya tsaf domin ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, zaben mai inganci kuma mai tsabta. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China