in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotu a Najeriya ta ba da umarnin tsare alkalin alkalan kasar
2019-02-14 09:43:29 cri

Kotun da'ar ma'aikatan tarayyar Najeriya ta ba jami'an tsaro umarnin tsare Walter Onnoghen, dakataccen alkalin alkalan kasar dake fuskantar tuhuma kan rashin bayyana kadarorin da ya mallaka.

An ba da umarnin tsare Walter Onnoghen ne, yayin zaman kotun na jiya Laraba a birnin Abuja.

Ana tuhumar Walter Onnoghen ne saboda mallakar asusun banki na sirri dake dauke da miliyoyin daloli.

Shugban kotun Danladi Umar, ya umarci mukaddashin babban sufeton 'yan sandan kasar da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya, su tsare alkalin alkalan kafin zaman kotun na gobe Juma'a.

An fara tuhumar Walter Onnoghen ne bayan wata kungiyar kare hakkokin al'umma ta shigar da korafi gaban kotun da'ar ma'aikatan, inda take zarginsa da mallakar wasu asusun ajiya da bai bayyana ba, wanda kuma shi da kansa yake zuba kudi a cikinsu.

Ana zargin ana tafiyar da asusun ne bisa hanyoyin da suka sabawa tsare gaskiya da dokar da'ar ma'aikata ta kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China