in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: An samu gagarumin ci gaba a harkokin kiwon lafiya a yankuna masu fama da talauci
2019-02-13 20:24:43 cri

Mataimakin darekta mai kula da harkokin kiwon lafiya a hukumar kula da lafiya ta kasar Sin Jiao Yahui ta bayyana cewa, an samu gagarumin ci gaba a harkokin kiwon lafiya a yankunan kasar masu fama da talauci, inda aka daga matsayin sama da asibitoci 400 zuwa manyan asibitoci.

Jami'ar wadda ta bayyana hakan yayin taron manema labarai, ta ce yanzu haka sama da asibitoci 30 a wadannan yankuna za su iya samar da kulawar lafiya yadda ya kamata kamar sauran manyan asibitoci dake kasar.

Jiao ta kara da cewa, marasa lafiya a dukkan yankuna masu fama da kangin talauci, za su iya samun kulawa bisa tsarin amfani da na'urorin zamani a kananan asibitocin dake yankunansu.

Jami'ar ta danganta wannan ci gaba da aka samu kan irin taimako da asibitoci masu inganci dake kasar suka ba da a 'yan shekarun da suka gabata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China