in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bill Gates: Sin babbar mai taimakawa cigaban duniya ce
2019-02-13 14:11:45 cri
Hamshakin attajirin nan Bill Gates, kuma jami'in gudanarwar gidauniyar bada tallafi ta Bill da Melinda Gates, ya fada a jiya Talata cewa, an samu gagarumin cigaba wajen yaki da talauci da kuma cututtuka a duniya a shekarar 2018, kuma kasar Sin ita ce babbar mai bada gudunmowa wajen cimma wannan nasarar da aka samu.

A wani jawabin faifan bidiyo ta aka watsa ta kafar watsa labarai na kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Gates ya ce, a cikin shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta tsame sama da mutane miliyan 800 daga kangin talauci, kuma ta kasance kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya. A yanzu haka, kasar ta dukufa wajen ganin ta agazawa sauran sassan duniya wajen magance manyan kalubalolin dake addabarsu.

Gates ya gana da wani kwararren masanin kimiyyar kasar Sin wanda yake kokarin kirkiro sabbin magungunan da za'a iya amfani da su wajen magance wasu nau'in cutuka kamar tarin fuka wato tarin tibi wanda ya fi shafar mutane masu karamin karfi, kuma ya tattauna da wasu sinawa abokan hulda wadanda suke musayar ilmi kan irin cigaban da kasar Sin ta samu, domin kasashen Afrika su amfana wajen samun muhimman cigaba a wasu fannoni masu muhimmanci kamar bangaren kyautata sha'anin kiwon lafiya da yaki cutuka masu saurin kisa kamar cutar zazzabin malariya, da kuma inganta fannin sauye-sauye a aikin gona.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China