in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaya kamfanin kasar Sin ya gama samar da kayan more rayuwar al'umma mafi girma a kasar Mozambique?
2019-02-13 11:58:45 cri

A watan Nuwamban shekarar 2018, kamfanin shimfida titi da gina gada ta kasar Sin, wato CRBC ya gama aikin samar da kayan more rayuwar al'umma mafi girma a kasar Mozambique, wato gadar Maputo da hanyoyin mota dake hada gadar da sauran hanyoyi. Sakamakon haka, an samu saukin zirga-zirga tsakanin gabobi biyu na sashen gabar tekun Maputo, ta kuma zama wata muhimmiyar hanyar dake ratsa kasar daga arewa zuwa kudu, har ma zuwa kasar Afirka ta kudu. Tabbas za ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa kasar Mozambique.

A shekarar 2012 aka rattaba hannu kan kwangilar gina gadar Maputo, sannan a shekarar 2014 aka kaddamar da aikin da aka kammala shi a watan Nuwamban shekarar 2018. Dimbin ma'aikatan kamfanin CRBC ne suka bayar da gudummawarsu wajen yin aiki. Har ma wasu ma'aikata Sinawa daga cikinsu ba su koma gidajensu dake nan kasar Sin ba tsawon wasu shekaru. Yanzu ga labarun dake faruwa a lokacin da ake gina gadar.

"A lokacin da na gama karatu daga jami'a, ina son fita waje domin bude ido. A wancan lokaci, ina da kuruciya, ina son zuwa ko ina, ciki har da nahiyar Afirka. Sakamakon haka, da na fara aiki a kamfanin CRBC, aka tura ni zuwa Afirka. Har yanzu ban koma gida ko sau daya ba."

Mr. Bai Pengyu, babban direktan ofishin kamfanin CRBC dake kasar Mozambique ya dade yana aiki a Afirka. Ba da dadewa ba bayan ya samu aikin yi a kamfanin CRBC, ya fara aiki a kasashen Habasha da Kenya da Angola da Rwanda da kuma Mozambique tun daga shekarar 2001 har zuwa yanzu.

A shekarar 2012 ce Mr. Bai ya fara aiki a kasar Mozambique domin gudanar da aikin ginin gadar Maputo.

"Idan ka duba taswira, za ka iya ganin cewa, a kudancin Mozambique, akwai wani sashen gabar teku da ba a iya ratsa shi zuwa yankin kudu. Wannan yankin na kudu yana makwabtaka da kasar Afirka ta kudu. Sakamakon rashin samun ci gaban yankin kudancin Mozambique ne gwamnatin kasar ta tsara shirin gina wata gada."

Gadar ta Maputo mai tsawon kilomita 3 ta ketare sashen gabar tekun Maputo dake hada garin Maputo, babban birnin kasar Mozambique da yankin Katembe dake kudancin kasar. Kafin a kaddamar da gadar, ana amfani da kananan jiragen ruwa da ba su iya daukar kaya ko mutane da yawa, inda ake bata tsawon lokaci yayin da ake ketare sashen gabar tekun Maputo. Idan an tuka mota daga arewa zuwa kudu kuwa, tsawon hanyar da ake bi ya kai kilomita 160. Amma yanzu, idan an tuka mota daga arewa zuwa yankin kudancin sashen gabar tekun Maputo, ana bukatar wajen minti 10 ne kawai.

Ba gina wannan gada kadai kamfanin kasar Sin ya yi ba, har ma ya shimfida wata hanyar mota mai tsawon kilomita 180 dake hada birnin Maputo da yankin kudancin kasar Mozambique dake hade da kasar Afirka ta kudu. Sakamakon hakan, yanzu awa 1 kadai matukan mota ke bukata daga Maputo zuwa kasar Afirka ta kudu, maimakon awa 4 da suke shafewa a da.

Mr. Bai ya bayyana cewa, matsala mafi tsanani da suka gamu da ita a lokacin da ake gina gadar ita ce, matsalar kaurar mazauna wurin. Bisa shirin da aka tsara, an gina wannan gada ne a wasu unguwannin mazauna. Sabo da haka, dole ne a lokacin da aka fara gina gadar, aka kuma yi aikin kaurar da mazauna wurin.

"Bisa kokarin da ma'aikatan kamfani da kuma hukumomin gwamnatin wurin suka yi, wannan aiki bai kawo illa ga zaman rayuwar mazauna wurin ba, domin kamfanin CRBC ya yi hadin gwiwa da gwamnatin wurin, inda suka sayi wani yankin dake karkarar birnin Maputo, kuma suka samar musu da wutar lantarki da ruwan sha da gidajen kwana da makaranta da kuma ofishin 'yan sanda da dai makamatansu."

An bayyana cewa, bayan kaddamar da gadar, a cikin gajeren lokaci aka ga yadda take taka rawa ga ci gaban yankin da ke kudancin kasar Mozambique. Alal misali, a lokacin da ake murnar bikin Kiresti na bara, mutanen kasar Afirka ta kudu wajen dubu 20 ne suka bi hanyar da aka shimfida dake kudancin kasar Mozambique domin shakatawa a yankin, maimakon dubu 5 dake bi kafin aikin. Bugu da kari, yanzu a karshen mako, mazauna birnin Maputo da yawa kan tuka mota su je shakatawa a kasar Afirka ta kudu.

Yanzu, a lokacin da yake daukar nauyin tabbatar da yin amfani da gadar da kuma ingancinta, kamfanin CRBC ya kuma tsara shirin yin hadin gwiwa da hukumar wurin, wajen bunkasa yankin kudancin kasar, har ya kai ga zama wani yankin zamani na samun ci gaba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China