in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: An samu ci gaba a fannoni biyar bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya"
2019-02-13 11:12:59 cri

Kasar Sin za ta shirya taron koli karo na biyu na hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" a watan Afrilu na bana. Qian Keming, mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin ya bayyana a jiya Talata, cewar yanzu ana raya ayyukan da shawarar ta shafa yadda ya kamata bisa niyyar kara ingancinsu.

Qian ya fadi hakan ne yayin taron manema labaran da aka yi a ranar, inda ya ce, an habaka ayyukan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya bisa shawarar a shekarar 2018, kuma ingancinsu ya kara kyautatuwa. Na farko dai, an kara saurin cudanyar cinikayya. Sin da kasashe 9 sun daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwar raya kasuwanci ta Intanet. Jimillar cinikayya a tsakanin Sin da kasashen da shawarar ta shafa ta karu da kashi 16.3 cikin dari.

Na biyu, ana cigaba da inganta hadin gwiwar zuba jari. Yawan jarin da kasashen da shawarar ta shafa suka zubowa Sin ya kai dala biliyan 6.08, yayin da yawan kudaden da Sin ta zuba musu kai tsaye ya kai dala biliyan 16.27.

Na uku, an kammala wasu manyan ayyukan more rayuwa. Kamar gadar zumunci tsakanin Sin da Maldives da ke kasar Maldives da kuma layin dogo tsakanin Addis Ababa da Djibouti sun fara aiki.

Na hudu, ana gaggauta raya tsarin cinikayya maras shinge.

Na karshe shi ne ana kyautata tsarin hadin kai. Kamar Sin da Thailand da Kenya sun kafa kungiyar tuntubar cinikayya bi da bi, Sin da Kuwait da Jordan sun kafa kungiyar kula da zuba jari bi da bi, baya ga kafa tsarin hadin gwiwar samar da hidimomin cinikayya tare da kasashe bakwai. (Kande)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China