in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce ta shiryawa gudanar da zabe cikin lumana
2019-02-13 10:58:01 cri
Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce tana hada hannu da sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da ganin an gudanar da zaben kasar dake karatowa cikin kwanciyar hankali da lumana.

Da yake gabatar da jawabi ga shugbannin hukumomin tsaro da na jam'iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a birnin Minnan jihar Niger dake arewacin kasar, kakakin rundunar Godwin Nwabodo, ya ce wajibi ne kowa ya kiyaye dokokin gudanar da zabe.

Godwin Nwabodo ya yi kira ga dukkan 'yan siyasa da sauran masu tsaki su kiyaye ka'idoji da dokokin zabe na kasar.

Ya kara da cewa, a shirye 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro suke su tabbatar da ganin an gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Har ila yau, ya ce jami'an tsaro za su tabbatar da kare hakkokin masu kada kuri'a, saboda sun shirya daukar mataki kan masu ta da fitina. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China