in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mukaddashin ministan tsaron Amurka ya ziyarci Iraki
2019-02-13 10:39:25 cri

Mukaddashin ministan tsaron kasar Amurka Patrick Shanahan ya ziyarci kasar Iraki jiya Talata, inda ya yi shawarwari tare da firaministan kasar Iraki Abdul-Mahdi a birnin Bagadaza kan batun yakar ta'addanci da hadin gwiwar bangarorin biyu ta fuskar tsaro.

Ma'aikatar tsaron kasar Amurka ta bayar da sanarwa a ranar, inda ta ce a cikin shawarwarin, an tabbatar da huldar hadin gwiwar Amurka da Iraki a fannin tsaro, wadda za ta mayar da hankali kan fafattakar kungiyar IS bisa goyon bayan kawancen kasa da kasa na yakar kungiyar IS mai tsattsauran ra'ayi.

A nasa bangaren, Mr. Abdul-Mahdi ya furta cewa, kasar Iraki na son ci gaba da hadin kai da Amurka wajen yakar ta'addanci, amma dole ne bangarorin biyu su girmama yarjejeniyar tsaro a tsakaninsu, kana aikin sojojin Amurka da ke kasarsa shi ne yaki da ta'addanci da ya taimaka wajen horar da sojojin tsaron Iraki kawai. A cewarsa, Iraki ba ta amince da kasancewar ko wane sansanin soja na waje a yankunanta ba. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China