in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin jarin wajen da aka zuba a kasar Sin ya karu cikin sauri
2019-02-12 19:16:21 cri

Yau Talata a nan birnin Beijing ma'aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin ta bayyana cewa, adadin sabbin kamfanonin da 'yan kasuwan kasashen waje suka kafa a nan kasar Sin a shekarar 2018 da ta gabata ya kai 60533, adadin da ya karu da kaso 69.8 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2017, kana adadin jarin wajen da aka yi amfani da su a shekarar ya kai kudin Sin yuan biliyan 885.61, adadin da ya karu da kaso 0.9 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2017. An lura cewa, a shekarar bara, wato shekarar 2018, kasashen duniya ba su samu isasshen jarin wajen da suke fatan samu ba, amma lamarin ba haka yake a kasar Sin ba, har adadin jarin wajen da ta samu ya karu matuka, lamarin da ya nuna cewa, harkokin kasuwancin kasar Sin na gudana yadda ya kamata, ganin yadda ta jawo hankalin 'yan kasuwan kasashen duniya matuka.

Game da batun yadda kasar Sin take yin amfani da jarin waje, ana iya fahimtar fiffikonsa daga fannoni uku:

Na farko, tsarin yin amfani da jarin waje yana kyautatuwa sannu a hankali, alkaluma na nuna cewa, a shekarar 2018 da ta wuce, adadin jarin wajen da aka yi amfani da su a bangaren kere-kere ya kai kaso 30.6 bisa dari, kana adadin da aka yi amfani da su a bangaren kere-keren fasahohin zamani ya kai kaso 35.1 bisa dari, wannan na nuna cewa, dalilin da ya sa 'yan kasuwan kasashen waje suka kara zuba jari a bangaren aikin kere-keren fasahohin zamanin kasar Sin shi ne domin suna iya samun riba mai tsoka a bangaren, saboda raya aikin kere-keren fasahohin zamani ya dace da manufar da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa yayin da take kokarin ingiza ci gaban tattalin arziki mai inganci da kuma kyautata tsarin sayayya a kasar.

Na biyu, adadin jarin da 'yan kasuwan kasashen waje suka zuba a yankunan dake tsakiya da yammancin kasar ya karu cikin sauri. A shekarar bara, gaba daya adadin jarin wajen da aka yi amfani da su a yankunan dake yammacin kasar ya kai kudin Sin yuan biliyan 64.6, adadin da ya karu da kaso 18.5 bisa dari, a yankunan dake tsakiyar kasar kuwa, adadin ya kai kudin Sin yuan biliyan 64.8, adadin da ya karu da kaso 15.4 bisa dari, an kuma samu wannan babban sakamakon ne saboda gwamnatin kasar Sin tana kara nuna goyon bayanta ga ci gaban yankunan. A halin da ake ciki, kasar Sin ta tsara wata sabuwar takardar jeren sana'o'in da take fatan 'yan kasuwan kasashen waje su kara zuba jari a kai, haka kuma za a tattauna a kan su, domin samun shawarwarin da suka dace, ana sa ran cewa, nan gaba yankunan tsakiya da yammacin kasar za su samu jarin waje kamar yankunan gabashin kasar suke samu a yanzu, ta yadda za a kara karfafa hadin gwiwa a fannin zuba jari dake tsakanin kasashen da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya, tare kuma da kafa manyan kamfanonin kasa da kasa. A fili take cewa, kasar Sin ta samar da karin damammaki ga 'yan kasuwan kasashen waje domin su kara zuba jari a kasar ta Sin.

Na uku, adadin jarin da 'yan kasuwan kasashe masu ci gaba suka zuba a kasar Sin ya karu matuka. Alkaluma sun nuna cewa, a shekarar 2018, adadin jarin da Birtaniya da Jamus da Koriya ta Kudu da Japan da Amurka suka zuba a kasar Sin ya karu da kaso 150.1 bisa dari ko kaso 79.3 bisa dari ko kaso 24.1 bisa ko kaso 13.6 bisa dari ko 7.7 bisa dari. Abu mafi jawo hankalin jama'a shi ne, duk da cewa, rigingimun cinikayyar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ya tsananta a bara, amma adadin jarin da Amurka ta zuba a kasar Sin yana ci gaba da karuwa, hakan ya nuna cewa, rigingimun bai yi wani tasiri ga kamfanonin Amurka ba ko kadan, har ma suna cike da imani ga kasuwar kasar Sin, wannan lamarin shi ma ya shaida cewa, babbar kasuwar kasar Sin wadda ke da masu sayayya da yawansu ya kai miliyan 1400 tana samar da muhimman damammakin ci gaba ga daukacin kamfanonin kasa da kasa a fadin duniya.

Makasudin zuba jari shi ne domin samun riba, a don haka idan kasar Sin ta kara bude kofa, ta kuma kara kyautata yanayin kasuwanci, tabbas ne jarin wajen da za a zuba a kasar zai karu cikin sauri. Babban jagoran kamfanin kera motoci na Tesla Elon Musk yana ganin cewa, da gaske ne kasar Sin ta dauki hakikanan matakan da suka dace yayin da take yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. Shugabar kamfanin IKEA reshen kasar Sin Anna Pawlak-Kuliga ita ma ta bayyana cewa, kokarin da gwamnatin kasar Sin take yi na kyautata yanayin kasuwanci ya burge ta kwarai. Wani jagoran kamfanin mai na kasar Birtaniya wato BP shi ma ya bayyana cewa, kamfaninsa zai bude gidajen sayar da mai sama da 1000 a kasar Sin a cikin shekaru biyar masu zuwa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China