in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Shanghai ya zama kan gaba wajen bude kofa ga ketare domin samun karin ci gaba
2019-02-12 15:55:02 cri

A rana ta farko da aka fara aiki bayan murnar bikin bazara, gwamnatin birnin Shanghai ta shirya taro kan yadda za a kara kyautata yanayin tattalin arziki da kasuwanci a birnin, inda aka fitar da wani sabon shirin dake kunshe da matakai 25 domin kokarin samun babban ci gaba.

A watan Maris na shekarar 2017, lokacin da yake tattauna ayyukan da ya kamata gwamnti ta yi tare da wakilan jama'ar birnin Shanghai, Xi Jinping ya nuna cewa, ba za ta rufe kofar kasar Sin ga ketare ba, kuma dole ne ta tsaya kan matsayin bude kofarta daga dukkan fannoni da kara bunkasa ciniki da kasashen waje da zuba jari ba tare da kafa shinge ba.

Bisa umurnin babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS, birnin Shanghai ya kara yin kokarin ba da hidima ga 'yan kasuwa da masu zuba jari na kasa da kasa. A watan jiya kawai, an kaddamar da babbar masana'antar farko a birnin Shanghai da kamfanin Tesla na kasar Amurka ya kafa a ketare. Bisa shirin da aka tsara, wannan masana'antar za ta samar da motoci masu aiki da wutar lantarki dubu dari 5 a duk shekara, wannan kuma shirin jarin waje mafi girma ne da aka kafa a birnin Shanghai a tarihi.

Mr. Elon Musk, jami'in farko na kamfanin Tesla ya ce, idan babu goyon bayan gwamnatin wurin, ba zai yiyu mu gina masana'antarmu mafi girma a Shanghai cikin sauri matuka ba. Tabbas wannan masana'anta za ta zama daya daga cikin masana'antunmu mafi kyau a duk duniya.

A 'yan shekarun baya, a lokacin da masana'antun dake samar da kayayyakin dake da nasaba da motoci suka kafu a yankin Lin'gang, sauran masana'antu ma sun kafu a kai a kai. A shekarar 2018, yawan kwangilolin jawo jarin waje a yankin Lin'gang na Shanghai ya karu da ninki 2. Sakamakon haka, yanzu ana hanzarta bude yankin Lin'gang.

Mr. Chen Jie, zaunannen mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin yankin Lin'gang na Shanghai ya ce, kwamitinsa ya kan bi manufar kara bude kofa ga ketare. Ta yaya za a iya kara bude kofar kasar Sin ga ketare har abada? Ita ce babbar bukatar da babban sakataren kwamitin kolin JKS yake da ita ga tattalin arzikin kasar. Kofar kasar Sin a bude take ga duk duniya har abada. Sabo da haka, a wajen yankinmu na Lin'gang, dole ne mu shigar da masu yin takara daga ketare, ta yadda za su iya yin takara da kamfanonin kasar Sin, da kuma yin hadin gwiwa tsakaninsu, domin kara kyautata karfinsu na samar da kayayyaki masu inganci.

A watan Satumban shekarar 2013, an kafa shiyyar cinikayya cikin 'yanci ta farko, wato shiyyar cinikayya cikin 'yanci ta Shanghai. Sabo da haka, a yayin da ake tattaunawa kan aikin gwamnati a tarukan NPC da CPPCC da ake yi a kowace shekara, babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kan mai da hankalinsa sosai kan yadda ake gina shiyyar.

Hukumar kula da harkokin bunkasa shiyyar cinikayya cikin 'yanci ta Shanghai tana tsayawa tsayin daka kan matsayinta na sabunta dokoki da ka'idoji. A cikin shekaru 5 da suka wuce bayan kafuwar shiyyar, ta riga ta fitar da sabbin sakamako 127 zuwa ga sauran yankunan kasar Sin, ta yadda take bayyana amfaninta na kasancewa kamar "wata gonar yin gwaji" kan harkokin yin gyare-gyare da bude kofa.

A cikin 'yan shekarun baya, an kafa farkon kamfanin dillancin sake yin inshora na kasar Sin, da kuma asibiti mai jarin waje na farko da dai makamatansu a Shanghai. Sannan a bara, gwamnatin birnin Shanghai ta fitar da "Sharuda 100 Wajen Kara Bude Kofa Ga Ketare" domin tabbatar da ganin an aiwatar da manufar bude kofar birnin daga dukkan fannoni, ta yadda za a iya tabbatar da ganin aikin gyare-gyare da na bude kofa sun amfanawa juna. Yanzu, bude kofarta, ta kasance kamar wani halin birnin Shanghai da ya fi jan hankalin waje, ya kuma sa birnin ya fi samun karfin gogayya a duk fadin duniya.

Manajan direktan kamfanin ABB Mr. Ulrich Spiesshofer ya ce, mun samu daman shigar da na'urori masu aiki da kansu da fasahohin AI a Shanghai, zai taimakawa birnin ya kasance a matsayin shugaban masana'antu masu aiki da kansu a duk duniya.

Kirkire-kirkire na sa kaimi ga samun ci gaba. A shekarar 2015, Xi Jinping ya bukaci birnin Shanghai da ya yi kokarin kasancewa cibiyar kimiyya da fasaha da yin kirkire-kirkire ta duniya, hakan zai samar da ci gaba da kuma kyakkyawar makoma ga birnin.

Ana kokarin yin kirkire-kirkire a birnin Shanghai yayin da ake kokarin kafa cibiyar kimiyya da fasaha da yin kirkire-kirkire ta duniya bisa tunanin jawabin shugaba Xi Jinping. An samu babban ci gaba a fannonin kafa na'urar X-ray mai karfi ta zamani, da manyan jiragen sama da Sin ta kera, da gabatar da sabbin magungunan yaki da ciwon sankara da sauransu.

Magatakardan kwamitin JKS na kamfanin Huahong na birnin Shanghai Zhang Suxin ya ce, babban sakatare Xi Jinping ya bada muhimmanci sosai ga raya hadaddiyar cibiyar sarrafa lantarki, da bukatar su da yin kokarin tabbatar da ikon mallakar ilmi da yin kirkire-kirkire kan kayayyaki masu lambar kira. Za su kara zuba jari ga yin kirkire-kirkire, ta hakan za a inganta fasahohin samar da kayyayaki da karfinsu na yin nazari.

Unguwannin mazauna su kasance kamar sassa mafi kankane ga zamantakewar al'umma. Xi Jinping ya furta aikin kula da harkokin zamantakewar al'umma sau da dama. Ya yi nuni da cewa, neman sabuwar hanyar kula da harkokin zamantakewar al'umma dake daidai da yanayin manyan biranen kasar na da nasaba da ci gaban birnin Shanghai. Ya kamata a tafiyar da harkokin birni kamar yin saka.

Bisa umurnin da Xi Jinping ya bayar, gwamnatin birnin Shanghai ta gabatar da wasu manufofi don inganta karfin hukumomin gwamnatin da yin kirkire-kirkire wajen sarrafa zamantakewar al'umma. A gun manyan taruruka biyu na birnin Shanghai na bana, an zartas da dokar rarraba shara, aikin rarraba shara zai jawo hankalin jama'a sosai.

Mazauni unguwar Hongchu ta birnin Shanghai ya ce, a wannan lokaci, akwai masu aikin sa kai da suka zo nan don taimakawa wajen rarraba shara. Ya ce dukkansu ne suka gudanar da wannan aiki, ba shi kadai ba.

A birnin Shanghai, ana aiwatar da shirin ayyuka na shekaru 3 na sarrafa birnin a fannoni daban daban, kuma an kara gabatar da manufofi da abin ya shafa masu dacewa da zamani. An kyautata tsarin sarrafa unguwannin birnin Shanghai, hakan ya sa kungiyoyi da dama suka kara mai da hankali ga jama'a. Kana an inganta na'urorin gano kayayyaki ta fasahohin zamani don raya birnin zuwa na zamani, da kuma neman tsarin inshora da kulawa ga tsofaffi don tinkarar batun tsofaffi.

Mataimakin babban sakataren gwamnatin birnin Shanghai kuma direktan kwamitin samun ci gaba da yin kwaskwarima na birnin Ma Chunlei ya ce, ya kamata mu bi tunanin jawabin shugaba Xi, da sa kaimi ga samun ci gaba bisa tunanin. Za a kara bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima, kana jami'an gwamnatin su kara yin kokari. Ta hakan za a iya gudanar da ayyukan birnin Shanghai yadda ya kamata, da yin kokarin cimma burin da aka tsara, da sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki, da kuma raya sabbin fannoni a birnin. (Sanusi Chen, Zainab Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China