in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin sojojin AU sun gana game da ficewarsu daga Somalia
2019-02-12 11:40:38 cri
Kwamandojin dakarun shirin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika AU dake aiki a Somalia, wato (AMISOM), sun fara taron yini 4 jiya Litinin a birnin Mogadishu, domin lalubo cikakken tsarin da za su bi wajen ficewa daga kasar.

Mataimakin shugaban shirin AMISOM Simon Mulongu, ya ce tsarin zai zayyana ayyukan da za a aiwatar karkashin sabon daftarin tsarin ayyuka na CONOPS, tare kuma da lokaci da kayayyakin da ake bukata na aiwatar da ayyukan.

Yayin jawabinsa na bude taron, Simon Mulongu ya ce suna bukatar yin amfani da 'yan kayayyakin da suke da shi wajen aiwatar da kunshin CONOPS domin taimakawa AMISOM sauke nauyin dake wuyanta na tsaron Somalia.

Daftarin CONOPS wanda tsari ne na ficewar AMISOM, shi zai bayyanawa sojojin AU ayyukan da za su yi tsakanin 2018 zuwa 2021.

Taron ya samu halartar kwamandojin shiyya wadanda suka jagoranci tawagar sojojin kasashen da suka ba da gudunmuwar soji ga shirin AMISOM da wakilai daga rundunar sojin Somalia da MDD da sauran abokan hulda.

Simon Mulongu ya bukaci kwamandojin da su bullo da tsarin ayyuka masu yiwuwa wadanda za su tabbatar da aiwatar da muhimman bukatun CONOPS. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China