in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara kokarin gina kyakkyawar duniya tare da sauran kasashen duniya
2019-02-11 20:33:27 cri

Yau Litinin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana a birnin Beijing, cewar a cikin wannan sabuwar shekarar da muke ciki, kasar Sin na fatan kara kokari tare da sauran kasashen duniya domin gina kyakkyawar duniya mai jituwa da wadata.

A yayin bikin bazara na bana, wanda ake yi don murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, shugabannin kasashen Amurka da Birtaniya da Japan da dai sauransu sun taya jama'ar Sin fatan alheri ta hanyoyi daban daban. Firaministan kasar Rasha Dmitry Medvedev kuwa ya ziyarci ofishin jakadancin Sin da ke Rasha don taya murnar bikin. Madam Hua ta yi wannan furuci ne yayin da take amsa tambaya game da batun.

Ban da wannan kuma Madam Hua ta ce, shugabannin kasashe da dama sun taya al'ummar Sin murnar sabuwar shekara da yi musu fatan alheri, sa'an nan sun jinjina babbar gudummawar da Sinawa ke bayarwa wajen kara azama ga bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasashensu. Lamarin da ya shaida tasirin al'adun gagajiyar kasar Sin, da amincewarsu ga ra'ayoyin al'adun gargajiyar Sin, da ma aniyarsu ta kara cudanya da hadin gwiwa tare da Sin.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China