Shugaban na Koriya ta kudu ya ce, zagaye na biyu na tattaunawar DPRK da Amurka zai kara matsawa zuwa mataki na gaba inda ake sa ran daukar kwararan matakai game da kawar da makaman nukiliya daga zirin Koriya, da gyara alakar dake tsakanin Amurka da DPRK, da batun wanzar da zaman lafiya a zirin Koriya, wadanda dama su ne manyan batutuwan da aka amince da su tun a zagayen farko na tattaunawar tsakanin Washington da DPRK. (Ahmad Fagam)