in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta inganta rokar Long March-6 domin karuwar bukatun kasuwanci
2019-02-11 16:07:20 cri

Kasar Sin ta sanar a yau Litinin cewa, tana kokarin inganta rokar Long March-6, ta yadda za a kara mata wasu rokoki 4 domin kara karfinta na daukar abubuwa.

A cewar cibiyar fasahar kera kambunan sararin samaniya ta Shangahai, za a harba rokar zuwa sararin samaniya ne a shekarar 2020, karkashin kulawar hukumar kula da fasahohi da kimiyyar kere-keren sararin samaniya ta kasar Sin, wadda ta kera rokar.

Rokar wadda ta fi gudanar da ayyukan kasuwanci, ta kammala gwaje-gwaje 2 da ta yi a sararin samaniya ne a watan Satumban shekarar 2015 da Nuwamban shekarar 2017, inda a farko ta dauki taurarin dan Adam 20 yayin da a gwaji na biyu kuma ta dauki taurari 3. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China