Kim Eui-keum, kakakin fadar ta Blue House, ya shedawa 'yan jaridu cewa, shugabannin Koriya ta kudu da na Amurkar za su tattauna ne game da batun zagaye na biyu na taron tattaunawar DPRK da Amurka wanda ake sa ran shiryawa a nan gaba, yana mai cewa, har yanzu ba'a bayyana takamamman lokaci ba, amma a cewarsa nan ba da jimawa ba za'a kammala shirya taron ganawar.
Moon da Trump ana sa ran za su yi musayar kalaman ne ta wayar tarho a nan gaba kadan. (Ahmad Fagam)