in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
SADC da MDD sun tattauna hanyoyin warware rikicin siyasar Zimbabwe da DRC
2019-02-11 10:00:33 cri
Shugaban kungiyar raya cigaban kasashen kudancin Afrika (SADC) kana shugaban kasar Namibia Hage Geingob a ranar Lahadi ya gayyaci babban sakataren MDD Antonio Guterres domin tattauna hanyoyin warware dambarwar siyasa a kasashen Zimbabwe da jamhuriyar demokaradiyar Kongo DRC.

A wata sanarwar da aka fitar daga ofishin shugaban kasar Namibian, Geingob ya ce, ya gayyaci babban jami'in MDD ne a gefen taron kungiyar tarayyar Afrika AU a Habasha domin yi masa karin haske game da halin da ake ciki a kasashen Zimbabwe da DRC.

"Da safiyar nan ne muka kammala tattaunawa da sakatare janar na MDD. Mun tattauna game da yanayin siyasar da ake ciki a DRC, Zimbabwe da yankin kudancin Afrika baki daya. Mun cimma matsaya game da aikin hadin gwiwa tsakanin SADC da MDD domin inganta yanayin shugabanci da kyautata rayuwar al'ummar shiyyar SADC," in ji Geingob.

A halin yanzu Zimbabwe tana fuskantar boren al'ummar kasar sakamakon matsanancin tashin farashin kayayyaki da tsadar rayuwa dake addabar talakawa masu karamin karfi a kasar, lamarin da ya tunzura jama'a suka fita titunan kasar don yin zanga zangar adawa da kara farashin man fetur da aka yi a kasar a watan jiya.

Haka zalika ana zargin sojojin kasar da aikata laifukan take hakkin bil adama a kasar ko da yake shugaban kasar Zimbabwen Emmerson Mnangagwa yana cigaba da bayyanawa takwarorinsa dake shiyyar cewa komai yana tafiya daidai a kasarsa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China