in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin kudin shigar da aka samu wajen yawon shakatawa yayin bikin bazarar Sinawa ya zarta yuan biliyan 500
2019-02-11 09:59:12 cri

Bisa alkaluman da cibiyar nazarin yawon shakatawa ta kasar Sin ta samu, an ce, yayin bikin bazara na gargajiyar kasar Sin na bana wato shekarar 2019, adadin Sinawa wadanda suka yi yawon shakatawa domin bude ido a fadin kasar ya kai miliyan 415, adadin da ya karu da kaso 7.6 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara. A sanadin haka, adadin kudin shigar da aka samu daga bangaren ya kai kudin Sin yuan biliyan 513.9, haka kuma adadin ya karu da kaso 8.2 bisa dari idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin a bara. An kuma lura cewa, ana gudanar da kasuwar al'adun yawon shakatawa lami lafiya a kasar ta Sin.

Yayin bikin bazara na gargajiyar kasar Sin, Sinawa sun fi son fita waje yawon shakatawa domin bude ido, a don haka an shirya ayyukan yayata al'adu a jere a yankuna 12 na kasar, misali birnin Beijing da lardin Shanxi da jihar Mongolia ta gida da sauransu, kana an shirya ayyukan yayata al'adun gargajiyar kasar Sin a sauran larduna kamar su Anhui da Guangdong, ban da haka kuma, wasu Sinawa sun fi son shiga wuraren adana kayayyakin tarihi yayin bikin bazarar.

A shekarar 2019, tasiri bikin bazarar kasar Sin ya kara habaka a sauran kasashen duniya, inda har aka shirya ayyukan taya murnar bikin sama da 1500 a birane 396 na kasashe ko yankuna 133 a fadin duniya baki baya, ta hakan, an samu babban sakamako wajen yayata al'adun kasar Sin ga sauran kasashen duniya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China