Ministan kula da harkokin tattara bayanan sirri na kasar Iran, Mahmoud Alavi, ya ce Iran ta tsare mutane 7 dake da alaka da kungiyar IS.
Mahmoud Alavi ya ce, an gano tare da tsare wasu mutane bakwai dake kitsa muggan ayyuka a daren ranar Juma'a.
Ya kara da cewa, an kuma cafke wasu karin mutane dake da alaka da kungyar, yana mai cewa, ma'aikatar tattara bayanan sirri na kasar za ta ci gaba da bibiyar zirga-zirgar 'yan kungiyar a cikin kasar.
Kasar Iran ta kara tsaurara matakan tsaro yayin da ake tsaka da bukukuwan murnar zagayowar ranar samun nasarar juyin juya halin kasar. (Fa'iza Mustapha)