in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin wadda take da masu yawon bude ido mafiya yawa sabon karfi ne ga duk duniya
2019-02-09 16:53:09 cri

A 'yan kwanakin baya, "sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar Sinawa" ta zama kalmar da ta kan bullo a cikin rahotonnin da kafofin watsa labaru na kasashen duniya suka wallafa. Alal misalai, shugabannin kasashen duniya sun gabatar da jawabansu na taya al'ummomin Sinawa murnar sabuwar shekara, sannan an ga launin ja da Sinawa suke so a wasu sanannun gine-gine na kasa da kasa. Wasu kafofin watsa labaru na kasa da kasa fiye da 200 sun kuma yada bikin kide-kide da raye-raye na murnar sabuwar shekara da babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin, wato CMG ya tsara a kasashensu, har ma ana iya ganin yadda ake murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar Sinawa a wasu gasannin kwallon kwando na maza da aka shirya a kasar Amurka, NBA. Sabo da haka, Mr. Lars Loekke Rasmussen, firaministan kasar Denmark ya ce, "bisa al'adar kasar Sin, idan an zuba jari a shekarar alade, za a iya samun riba. Sakamakon haka, bari mu ci gaba da zuba jari da yin cinikayya domin cin moriyar juna a wannan sabuwar shekara."

A lokacin da bikin bazara na murnar sabuwar shekara yake nune-nunen yadda Sinawa suke neman gama kai da jituwa tsakanin iyalai da abokai, bikin ya kuma kasance kamar wani muhimmin dandali, inda kasar Sin da karfin tattalin arzikinta yake kan matsayi na biyu a duk duniya take yin mu'amala da sauran kasashen duniya. Sakamakon karuwar tattalin arzikinta, yanzu yawon bude ido a ketare ya kasance daya daga cikin hanyoyin jin dadin hutu da Sinawa wadanda suka samu karin kudade da kuma suke jin dadin zamansu da tsaro suke zaba.

Bisa hasashen da wasu hukumomin yawon bude ido na kasar Sin suka yi, an ce, yawan Sinawa da suke yawon bude ido a ketare a lokacin hutun murnar sabuwar shekara zai kai fiye da miliyan 7, wato ya karu da 15% bisa na bara. Kasashen Thailand da Japan da kuma Indonesiya sun zama wuraren da Sinawa suka fi son kai ziyara. Olivia Ruggles-Brise wanda ke kula da manufofi da yada labaru a kungiyar sha'anin yawon bude ido ta kasa da kasa WTTC ya nuna cewa, yawan Sinawa wadanda suke da karfin biyan kudin yawon bude ido a ketare yana ta karuwa a kai a kai, wannan ya ciyar da kasuwannin yawon bude ido na Bangkok da na Jakarta wadanda suke kusa da kasar Sin gaba.

James Riley, wani shugaban kamfanin hotel na kasa da kasa ya ce, ya lura cewa, a baya, masu yawon shakatawa na kasar Sin sun fi mai da hankali kan yin sayyaya, amma a halin yanzu, suna mai da hankali sosai kan kara saninsu game da al'adun wurin da suka je yawo.

Domin janyo hankulan masu yawon shakatawa na kasar Sin, wadanda suka tafi kasar Japan a lokacin hutun bikin bazara, wasu kamfanonin yawon shakatawa na kasar Japan sun tsara shirye-shiryen yawon shakatawa dake shafar al'adun kasar Japan, kamar su abincin Japan, fasahar samar da shayin ti, fasahar sa furanni cikin kwalaba da kuma wasan sumo da dai sauransu. A kasar Thailand kuma, gwamnatin kasar ta tsawaita lokacin amfani na bizar da suka wuce lokaci a watan Janairu zuwa karshen watan Afrilu, ta kuma kafa hanyar musamman ga masu yawon shakatawa na kasar Sin a filin jiragen sama, da tsara shirin yawon shakatawa na musamman ga masu yawon shakatawa 'yan kasar Sin. A wasu kantunan kasar Indonesia kuma, ana sayar da kayyayakin musamman da Sinawa suke son a lokacin bikin bazara, kamar ambula mai launin ja da a kan sa kudin kyauta da dai sauransu.

Ko shakka babu, sha'anin yawon shakatawa ya kasance muhimmin bangaren inganta bunkasuwar tattalin arzikin kasa da kasa, a lokacin nan na musamman, wato farfadowar tattalin arzikin duniya bai kai hasashen da aka taba yi ba. A shekarar 2018, adadin mutanen da suka je yawon shakatawa ya kai biliyan 1.4, wanda ya kai wani sabon matsayi a wannan fanni. Kana ya wuce hasashen da hukumar yawon shakatawa ta yi, cewar, adadin masu yawon shakatawa a duniya zai kai wannan matsayi a shekarar 2020. Kuma masu yawon shakatawa na kasar Sin sun ba da muhimmiyar gudummawa a wannan fanni. A shekarar 2014, adadin Sinawan da suka tafi yawon shakatawa a kasashen ketare ya wuce miliyan dari daya, wanda shi ne karo na farko, sa'an nan, a shekarar 2018, adadin wadanda suka tafi yawon shakata a kasashe da yankuna kimanin 157, ya kai miliyan dari daya da arba'in. Haka kuma, cikin shekaru 5 da suka gabata, adadin masu yawon shakatawa na kasar Sin wadanda suka tafi ketare ya ci gaba da zama mafi yawa a duk fadin duniya.

Ana iya cewa, masu yawon shakatawa na kasar Sin sun ba da babbar gudummawa ga karuwar tattalin arziki a wuraren da suka tafi. A shekarar 2018, adadin Sinawa da suka je yawon shakatawa a kasar Indonesia ya kai miliyan 2, wanda ya kasance mafi yawa idan aka kwatanta da na sauran kasashen duniya. Dangane da wannan lamari, ministan harkokin yawon shakatawa na kasar Indonesia Arief Yahya ya bayyana cewa, bisa kididdigar da kasar ta yi, ko wane mai yawon shakatawa na Sin ya iya kashe dallar Amurka 1100, wanda ya tabbatar da karuwar kudin shiga a kasar.

Alkaluman da aka samu daga kasar Birtaniya sun nuna cewa, a shekarar 2017 Sinawa masu yawon shakatawa sun kashe kudin da yawansu ya zarce dalar Amurka miliyan 900 a kasar Birtaniya, jimilar da ta karu da kashi 35% bisa ta shekarar 2016. Hakan ya sa hukumar yawon shakatawa ta kasar Birtaniya ta mai da kasar Sin a matsayin "kasar da aka fi samun masu yawon bude ido masu kudi".

Ban da samar da masu yawon shakatawa ga kasashe daban daban, kasar Sin ita kanta, na daya daga cikin manyan kasuwannin yawon bude ido. Majalisar sana'ar yawon shakatawa ta duniya ta taba gabatar da wani rahoto kan yanayin yawon shakatawa a manyan birane 72 na kasashe daban daban, inda ta sanya biranen kasar Sin irinsu Beijing, Shanghai, da Shenzhen, cikin jerin manyan kasuwannin yawon shakatawa guda 10 na duniya.

Haka zalika, yayin da kasar Sin ke kokarin kara bude kofarta ga kasashen waje, sana'ar yawon shakatawa, bisa matsayinta na wani bangare na aikin hadima da ciniki, ita ma ta zama wani fannin da ake kokarin gudanar da manufar bude kofa. Ga misali, tun daga ranar 1 ga watan Yulin bara, kasar Sin ta kaddamar da sabbin manufofi masu alaka da aikin yawon shakatawa a wasu larduna da birane 17 na kasar, inda aka yi gwajin samar da izinin shiga kasar don samun jinya, da samar da damar wuce wasu yankunan kasar ba tare da bukatar samun izinin shiga kasar ba cikin kwanaki 6, da kyautata tsarin sanya ido kan ziyarar tsallake kan iyakar kasa ta hanyar tuka mota, da baiwa kamfanoni masu kula da aikin yawon shakatawa na kasashen waje damar hadin kai da takwarorinsu na kasar Sin, da dai makamantansu. Sa'an nan a bangaren kafa yankin ciniki mai 'yanci mai halayyar musamman ta kasar Sin, kasar ta sanar da niyyarta ta mai da tsibirin Hainan dake kudancin kasar zama wata cibiyar kasuwanci da yawon shakatawa, inda za a karbi baki na kasashe daban daban. Duk wadannan manufofi za su zama dandali mai kyau ga yunkurin hadin kan Sin da kasashen waje.

Yadda Sinawa suke yawon shakatawa a kasashen waje a farkon wannan shekarar da muke ciki, ya zamanto wani mafari mai kyau ga shekarar 2019, wadda aka lakaba mata "shekarar hadin gwiwa a fannin yawon shakawata tsakanin kasashen Laos, New Zealand, kasashe tsibirun dake cikin tekun Pasific, da kuma kasar Sin". A zamanin da muke ciki na samun dunkulewar duniya, Sinawa da ke kai-kawo a kasashe daban daban suna musayar al'adu, da dandanon abubuwa masu halayyar musamman na kasashe daban daban, inda a sa'i daya suke nuna karamci, kuzari, da kuma sake imanin da kawunansu. (Sanusi Chen, Bello Wang, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China