in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin manya a kasar Sin zai iya karuwa daga shekarar 2025
2019-02-09 16:20:40 cri

Wani rahoto da kwalejin nazarin aikin likita ta Peking Union Medical College da hadin gwiwar kungiyar kula da tsoffi ta Chinese Aging Well Association suka fitar, ya ce akwai yuwuwar kasar Sin ta fuskanci karuwar adadin manya da suka kai shekaru 80 ko suka zarce hakan, daga shekarar 2025 zuwa 2050.

Rahoton wanda ya bada misali da wani rahoton da MDD ta wallafa mai taken "Hasashen yawan al'ummar duniya: Bitar 2017", Ya ce ya zuwa shekarar 2017, adadin manya da shekarunsu ya kai 80 ko ya zarta hakan, ya kai miliyan 26 a kasar Sin, adadin da ya kai kaso 1.8 na jimilar al'ummar kasar. Wanda kuma zai karu da kaso 2 a shekarar 2025, sannan ya harba zuwa kaso 8 a shekarar 2050.

Galibin al'ummar kasar za su kasance wadanda shekarun suka ja ya zuwa 2026, inda fiye da kaso 14 na al'umma za su kasance masu shekaru 65 ko fiye. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China