Ranar 10 ga watan Fabrairu rana ce ta ma'aikatan diflomasiyya ta kasar Rasha, don haka cikin sakonsa na taya murna, shugaba Putin ya ce, a halin yanzu, ana fuskantar gagarumin kalubale ta fuskar tsarin kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa. Ya ce, ya kamata Rasha ta sauke nauyin dake wuyanta a fannin diflomasiyya, ciki har da kare ka'idojin dokar kasa da kasa da goyon bayan MDD, da kuma warware matsalar ta'addanci cikin hadin gwiwar dake tsakaninta da gamayyar kasa da kasa. Ya kuma kara da cewa, Rasha za ta ci gaba da inganta yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar Syria, tare da dukufa wajen warware sauran matsalolin kasar ta hanyar diflomasiyya. (Maryam)