Vera Songwe ta ce idan za a yi la'akari da adadin, 'yan ci rani miliyan 23 su rubanya adadin al'ummar kasar Tunisia, sannan sun kusa yawan al'ummar kasar Ivory Coast, wanda nauyi ne yanzu akan nahiyar.
Jami'ar ta bayyana haka ne yayin jawabinta a taron majalisar zartaswar AU dake gudana a hedkwatar kungiyar, wanda aka yi wa taken, 'yan gudun hijira da masu dawowa gida: lalubo mafita mai dorewa ga daidaitar al'umma a Afrika.
Shugabar ta bukaci shugabannin nahiyar su hada hannu wajen magance matsalolin dake haifar da rashin matsuguni ga matasa a nahiyar.
Ta ce tambaya a gare su wato shugabannin Afrika ita ce, yadda a matsayinsu na kungiya za su samar da nahiyar da suke muradi, idan za su rika barin matasa da 'yan mata suna kokawa a sansanoni, ba tare da sun jin kunyar hakan ba. (Fa'iza Mustapha)