in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Huawei ya yi watsi da zargin da jakadan Amurka ya yi masa, tare da kare nagarta da tsaronsa
2019-02-08 16:20:30 cri

Wakilin kamfanin Huawei a kungiyoyin Tarayyar Turai Abraham Liu, ya yi kakkausar jawabi, inda ya yi watsi da fargabar da ake yadawa game da kamfanin.

Yayin jawabinsa a jiya da dare, a wani dakin taro a birnin Brussels mai dauke da mahalarta sama da 100, galibinsu Turawa, Abraham Liu ya kare babban kamfanin fasahar na kasar Sin.

Abraham Liu, ya ce a baya-bayan nan, wasu kasashe da 'yan siyasa sun sha sukar kamfanin, inda ya ce sun kadu da zarge-zargen marasa tushe bare makama.

Abraham Liu, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban kamfanin Huawei a yankin Turai, ya bada misali da jawabin Jakadan Amurka a Tarayyar Turai Gordon Sondland, wanda ya ce wani dake zaune a Beijing zai iya amfani da tsarin sadarwa na 5G wajen karbe ikon wata mota dake kan titi, har ma ya kai ga kashe direbanta. Tsokacin da wakilin ya bayyana a matsayin rainin hankali, musamman ga masana fasaha a fadin duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China