in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda Fasaha Ta Sake Fasalin Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa
2019-02-05 20:29:06 cri

Yayin bikin kade-kade da raye-raye na Litinin, 4 ga watan, wanda a yanzu ya zama na al'ada, da a kan shafe tsawon sa'o'i 4 ana watsawa a kafefen yada labarai a ranar jajibirin bikin Bazara, wanda kuma ya fi kowanne shirin nishadi na duniya samu masu kallo, wani shirin barkwanci da aka yi wa lakabi da 'Platform' ya bayyana labaran wasu ma'aurata 4 dake kokarin zuwa mahaifarsu don haduwa da iyalansu yayin da ake hanzarin tafiye-tafiya. Ana ganinsa a matsayin lokacin bulaguro mafi girma a duniya, inda ake tafiye tafiye kusan miliyan 40 cikin fadin kasar Sin a cikin kwanaki 40. Tafiya a wanna lokaci ka iya zama abu mai wahala.

Sai dai a yanzu kasar Sin ta shiga zamanin amfani da jirgin kasa mai saurin gudu, wanda ya yi gagarumin tasiri wajen rage cunkoson tafiye tafiye ga tsarin sufurin kasar, kuma mutane sun fi jin dadin tafiyar, wadda kuma ake yi cikin gajeren lokaci.

Baya ga yin tafiye tafiye cikin sauri, alamu sun nuna cewa Sinawa ba sa dakon kayayyaki a lokacin bulaguro. Kyaututtukan da ake ba abokan arziki da iyalai lokacin bikin bazara kan isa gida da wuri tun kafin masu bayar da kyautukan su tashi ta su tafiya, hakan ya samo asali ne daga ci gaba cikin sauri da aka samu a fannin sayayyar kayayyaki ta na'urori da sana'ar jigilar kayayyaki.

A bangare daya kuma, manyan kayayyakin fasaha na kara mamaye kasuwar kyaututtukan lokacin bazara. A cewar wata kididdiga daga ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, dubban sifiku irin na zamani nau'ika daban daban ne aka sayar cikin kankanin lokaci gabanin lokacin bikin bazarar ta hanyar siyayya ta naurorin zamani. Sauran kyaututtukan da suka yi fice sun hada da mutummutumin da ke iya shara da wanda ke debewa mutane kewa da na'urar markada kayan miya da jirage mara matuka da kayayyakin dumama jiki.

Alal hakika, amfani da na'urorin zamani na kara fadada tsakanin al'ummar Sinawa, ba ma kawai a yayin bukukuwa ba, har ma da sauran lokutan rayuwa na yau da kullum.

A yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin irin sa karo na farko da aka gudanar a watan Nuwamba a birnin Shanghai, inda kamfanonin Sin suka nuna sha'awarsu ga sayen hajojin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 57.8, kayayyaki irin su na'urar saisaita bugun zuciya mafi kankanta, da na'urar hada coffee, da na'urar dab'i samfurin 3D, da kuma kayan sawa masu dauke da na'urar dake gwada bugun zuciya, suna kan gaba cikin hajojin da Sinawa suka fi nuna sha'awar saya.

Dukkanin wadannan na nuna cewa, masu sayayya na kasar Sin na kara daga matsayin bukatunsu daidai da zamani. Ana ma iya cewa, hakan ne ya sanya sauran sassan duniya ke kokarin shiga a dama da su, a wannan kasuwa mai samar da dinbin riba.

A makon jiya, an gudanar da sabon zagaye na tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin bangaren Sin da na Amurka, tattaunawar da ta haifar da manyan nasarori. Nan gaba kadan kuma, ana fatan sake zantawa tsakanin sassan biyu, da nufin kawo karshen yarjejeniya tsakanin kasashen. Ana sa ran kara bude kofa sosai ga kasashen waje, zai fadada kasuwar hajojin da suka shafi na'urori na zamani a cikin kasar Sin, wanda hakan zai kara kyautata damar yin managarciyar rayuwa ga Sinawa a nan gaba. (Masu Fassarawa: Fa'iza Mustapha, Saminu Hassan, ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China