in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ya yi alkawarin tattaunawa da matasa masu zanga zangar tattalin arziki a kasar
2019-02-07 16:23:24 cri
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya sanar a jiya Laraba cewa, kofar tattaunawarsa a bude take da matasan kasar masu zanga zanga.

A yayin zantawa da 'yan jaridu a Khartoum al-Bashir ya ce, wadanda suke zanga zanga a titunan kasar wasu mutane ne da aka rene su a daidai lokacin da kasar ke kan ganiyarta na cin gajiyar albarkatun man fetur inda kuma kwatsam sai al'amurra suka sauya a sanadiyyar rikicin tattalin arziki da ya afkawa kasar.

Yayin da wasu ke zargin ballewar da Sudan ta kudu ta yi shi ne ummul aba'isin da ya haddasa rikicin tattalin arzikin kasar ta Sudan, al-Bashir ya ce, wasu matakai da dama da gwamnati ta dauka su ne suka harzuka matasan kasar ta Sudan.

Sudan ta jima tana fama da tashe tashen hankula a tarihin kasar tun bayan samun 'yancin kanta. Karkashin wata yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2005, shi ne ya haifar da ballewar sashin kudancin kasar, wacce ta haifi sabuwar kasar Sudan ta kudu a shekarar 2011.

Ballewar kasar Sudan ta kudu ya haifar da babban gibi wajen karayar tattalin arzikin kasar. Mafi muhimmanci daga cikin kalubalen da kasar ta fuskanta shi ne na hasarar kudaden shigarta daga bangaren albarkatun man fetur wanda ya zarta kashi 50 bisa 100 na hanyar samun kadaden shigar gwamnatin Sudan kana kashi 95 bisa 100 na hajar da kasar ke fitawar zuwa kasashen waje, kamar yadda kididdigar bankin duniya ya tabbatar da hakan. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China