"Ni da kaina na kirga gawarwakin mutane 15 maza da mata. Dukkansu an harbe su ne a kasuwa. Kuma ba masu dauke da makamai ba ne," wani mutum da ya ganewa idonsa faruwar lamarin shi ne ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Akwai bayanai dake cin karo da juna dangane wadanda suka aikata kisan. Wasu mazauna yankin sun zargi dakarun gwamnati da laifin hallaka mutanen, amma a nata bangaren gwamnatin ta ce an kashe mutanen ne a sanadiyyar barkewar tashin hankali tsakanin dakarun sojojin gwanati da mayakan 'yan aware masu dauke da makamai. (Ahmad Fagam)