Bangarorin masu adawa da juna a CAR sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Khartoum
A jiya Talata sassan dake yaki da juna a jamhuriyar Afrika ta tsakiya (CAR), suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya bayan kammala taron tattauanwar sulhu wanda gwamnatin kasar Sudan ta jagoranta a babban birnin kasar Khartoum.
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir, da takwaransa na jamhuriyar Afrika ta tsakiya Faustin Archange Touadera, wanda ya isa birnin na Khartoum tun da fari, sun halarci bikin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar. (Ahmad Fagam)