in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka fararen hula 4 a yanki masu magana da yaren Turanci a Kamaru
2019-02-06 15:46:30 cri
A kalla fararen hula 4 aka harbe har lahira a yankin jamhuriyar Kamaru mai fama da tashe tashen hankula a jiya Talata yayin da mayakan 'yan arewacin yakin suka fara kaddamar da hare hare da suka yiwa lakabi ""10-day lockdown," in ji hukumomin yankin.

"A kudu maso yammacin shiyyar, an kashe fararen hula 3 ciki har da wani dalibi guda a yankunan Buea, Tiko da Mutegene," in ji wani jami'in soji wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

"A babban garin arewa maso yammacin kasar wato Bamenda, an kashe wani matukin babur din haya wanda aka harbe har lahira," in ji jami'in. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China