Cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin Mr. Sadi ya nuna nadama ga kalaman da minista Jean de Dieu Momo ya yi ta kafar talabijin mallakar kasar.
Jami'in ya ce ministan harkokin hadin gwiwar kasar da kasashen waje, ya karbi bakuncin jakadan Isra'ila a kasar a ranar Litinin 4 ga watan nan na Fabarairu, inda ya bayyana masa takaicin gwamnatin kasar game da kamalan minista Momo, yana mai cewa ba da yawun gwamnati ya furta kalaman na batanci ba.
Rahotanni na cewa, minista Momo wanda ke aiki a ma'aikatar shari'ar kasar, ya kwatanta jami'iyyar adawar kasar ta CRM da Yahudawa, wadanda Hitler ya murkushe sakamakon dagawarsu. Mr. Momo ya yi wannan kalamai ne, yayin wata zantawa da wata kafar watsa labarai ta kasar. Jim kadan da hakan ne kuma, ofishin jakadancin Isra'ila dake kasar, ya bayyana matukar bacin ran sa da hakan, yana mai neman a baiwa Isra'ilan hakuri. (Saminu Hassan)