in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya nuna shakku game da fitar da rahoton Mueller
2019-02-04 13:40:25 cri
Yayin wata zantawa da kafar CBS ta Amurka a jiya Lahadi, shugaba Donald Trump na Amurka, ya ki tabbatar da yiwuwar bayyana rahoton Robert Mueller, game da binciken tsoma hannun kasar Rasha a zaben Amurka, wanda ya baiwa Trump din nasara. Shugaba Trump ya nace cewa, babban mai shari'a na Amurka ne zai yanke shawara game da yiwuwar bayyana rahoton.

Ya ce "ban san abun da rahoton zai fada ba, amma ba wani hadin baki, ba kokarin boye gaskiya, ba wani abu na daban, rahoton bai bayyana kowa a matsayin mai laifi ba. Duk da haka ina ganin abun kunya ne".

A cikin makon da ya gabata, mukaddashin babban mai shari'a na kasar Matthew Whitaker, ya ce binciken da ake yi game da kasar ta Rasha ya kusa kammala, duk da cewa ba a tabbatar da hakan daga ofishin lauyan musamman na gwamnatin kasar ba.

Mueller, wanda aka nada cikin watan Mayun shekarar 2017, na aikin bincike game da zargin rawar da Rasha ta taka, a babban zaben Amurka na shekarar 2016, da kuma bankado ko akwai wani hadin baki tsakanin tawagar yakin neman zaben shugaba Trump da Moscow, da dai sauran batutuwa masu nasaba. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China