"Sassan da ba sa ga maciji da juna sun cimma matsaya kan wasu muhimman batutuwa dake suke takaddama kansu, kamar batun rarraba madafun iko, da kammala kafa gwamnati bisa adalci a cikin wa'adin da aka diba, wanda aka dade ana tattaunawa kansa," in ji Attal-Mannan Bakheet, shugaban masu shiga tsakani na bangaren Sudan, shi ne ya bayyana hakan.
"Daftarin farko na yarjejeniyar za'a sanya hannu kansa ne da yammacin yau Lahadi a gaban shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir da takwaransa na CAR," in ji jami'in.
Bakheet ya kara da cewa, za'a sanya hannu kan yarjejeniyar karshe kan daftarin ne a Bangui a babban birnin CAR a ranar Laraba mai zuwa, a gaban shugabannin kasashen dake makwabtaka da CAR.
Tun a ranar 24 ga watan Janairu, Khartoum take ci gaba da karbar bakuncin tattaunawar zaman lafiya tsakanin gwamnatin CAR da bangarori 14 da ba sa ga maciji da juna a kasar. (Ahmad Fagam)