in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban Najeriya ya tsallake hadarin jirgi mai saukar ungulu
2019-02-03 15:29:32 cri
Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Yemi Osinbajo, ya tsallake rijiya da baya, bayan da jirgi mai saukar ungulu dake dauke da shi, ya yi saukar gaggawa a jiya Asabar a Kabba dake jihar Kogi.

Wata sanarwa da mai magana da yawunsa Laolu Akande ya fitar, ta ce jirkin helkwaftan mai cin mutane 6, na dauke da mataimakan shugaban kasar, da wasu masu tsaron lafiyarsa lokacin da hadarin ya auku, amma duk da cewa sassan jikin jirgin su kakkarye, babu wanda ya ji rauni sakamakon hadarin. Sanarwar ta kara da cewa, kwararru sun fara nazari domin zakulo musabbabin aukuwar lamarin.

Shi kansa mataimakin shugaban kasar ya bayyana ta shafinsa na twitter cewa, shi da dukkanin masu tallafa masa dake cikin jirgin sun kubuta lami lafiya, yana mai cewa masu tukin jirgin sun yi duk abun da ya dace domin kaucewa tasirin hadarin. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China