in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ba ta goyon bayan Amurka wajen janye jiki daga yarjejeniyar IRBM
2019-02-02 20:51:39 cri
Amurka ta sanar da dakatar da yarjejeniyar hana kera makamai masu linzami mai cin matsakaicin zango wato IRBM a jiya Jumma'a, sa'an nan, za ta fara aikin janye jiki daga yarjejeniyar a hukunce.

Dangane da wannan lamari ne yau Asabar, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana matakin a matsayin abin bakin ciki, yana mai cewa, a matsayin muhimmiyar yarjejeniya da Amurka da Rasha suka kulla kan aikin soja, yarjejeniyar IRBM na da ma'ana gaya wajen sassauta dangantakar dake tsakanin manyan kasashen duniya da kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa da ta shiyya-shiyya da kuma daidaita manyan tsare-tsaren kasashen duniya.

Ya kuma kara da cewa, kasar Sin ba ta goyon bayan Amurka wajen janye jiki daga yarjejeniyar, kuma tana fatan kasashen Amurka da Rasha za su yi shawarwari yadda ya kamata domin warware sabanin dake tsakaninsu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China