Maurice Kamto, ya bayyana gaban kotun sauraron kararraki na farko dake birnin Yaounde ne tare da wasu mambobin jam'iyyarsa 35, inda aka karanto musu tuhume-tuhumen da ake musu.
Jagoran lauyoyin jam'iyyar CRM Emmanuel Sim, ya ce sauran tuhume-tuhumen sun hada da yi wa kasa makarkashiya da hade kai ba bisa ka'ida ba da damun al'umma.
An shafe kimanin sa'a guda ana sauraron karar, kafin daga bisani a dage zaman zuwa ranar 15 ga watan Maris.
Tun a ranar Litinin 'yan sanda bangaren shari'a suke tsare da Kamto tare da mambobin jam'iyyarsa 117, bayan sun shirya wata zanga-zangar nuna kin jinin abun da suka kira da magudin zabe da yaki mara ma'ana a yankunan da ke da rinjayen masu amfani da Turancin Ingilishi. (Fa'iza Mustapha)