Ma'aikatar harkokin masana'antu da sadarwa ta kasar Sin ta fidda rahoto game da "yadda aka aiwatar da harkokin intanet da ayyukan ba da hidima masu alaka da shi a shekarar 2018". Rahoton da ma'aikatar ta fitar a jiya, ya ce a shekarar 2018, adadin kudin shiga na kamfanonin intanet da kamfanonin ba da hidimar intanet na kasar Sin ya kai yuan biliyan 956.2, adadin da ya karu da 20.3% idan aka kwatanta da na shekarar 2017.
Rahoton ya ce, a shekarar 2018, sana'ar intanet ta kasar Sin ta sami ci gaba matuka a fannin kirkire-kirkire, inda adadin kudin shiga a wannan fanni a birnin Guandong ya karu da kaso 26.5, birnin Shanghai kuma ya karu da kaso 20, yayin da na Beijing ya karu da kaso 25.2%, adadin da ya kasance kan gaba a duk fadin kasar Sin. (Maryam)