A yayin taron manema labaran da aka yi cikin hadin gwiwar Federica Mogherini da ministan harkokin wajen kasar Romania Teodor Melescanu bayan taron, Ms. Mogherini ta bayyana cewa, ministocin harkokin wajen mambobin kungiyar EU sun yi musayar ra'ayoyi kan yadda kungiyar EU za ta raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin. Ta ce, kasar Sin abokiyar kungiyar EU ce bisa manyan tsare-tsare, kuma muhimmiyar kasa ce cikin harkokin tattalin arziki da huldar ciniki da kuma batutuwan kasa da kasa da sauransu, lamarin da ya baiwa kunigyar EU damar raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin. Ta kara da cewa, EU tana son dukufa wajen habaka hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin.
Cikin shekarun baya bayan nan, kungiyar EU ta cimma nasarar karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin kan batutuwan da suka shafi fuskantar sauyin yanayi da kuma kiyaye yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran da wasu harkokin kasa da kasa.
Shi ma a nasa bangaren, Teodor Melescanu ya nuna cewa, mahalarta taron sun bayyana fatansu na inganta hadin gwiwar dake tsakaninsu da kasar Sin a fannonin warware matsalolin kasa da kasa da fuskantar sauyin yanayi da sauran wasu batutuwa. (Maryam)