in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Amurka sun bude sabuwar hanyar daidaita sabani a tsakaninsu
2019-02-01 17:10:52 cri

Daga ranar 30 zuwa 31 ga wata, an gudanar da shawarwari kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin tawagogin Sin da Amurka a birnin Washington, a karkashin jagorancin Mr. Liu He, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne mataimakin firaministan kasar da ma jagoran wannan shawarwari daga bangaren kasar Sin, da kuma Robert Lighthizer, wakilin kasar Amurka kan harkokin cinikayya.

Bisa ga daidaiton da shugabannin kasashen biyu suka cimma a yayin ganawarsu a kasar Argentina, sassan biyu sun tattauna batutuwan da suka jawo hankalin kasar Sin, ciki har da daidaita ciniki da musayar fasahohi da kariyar hakkin mallakar ilmi, da shingayen ciniki da ba na kudin kwastan ba, da aikin gona da sauransu, inda suka samu muhimmin sakamako. Ban da haka, sassan biyu sun kuma tabbatar da lokacin da za a gudanar da shawarwari na gaba.

Ba da sauki ba aka samu wannan sakamako, sai dai tuni aka tsinkaya shi. Isar tawagar kasar Sin a Amurka ke da wuya, sai fadar White House ta bayar da sanarwar nuna maraba, sa'an nan, bayan da aka kawo karshen shawarwarin, shugaba Trump na Amurka ya gana da Mr. Liu He, mataimakin firaministan kasar Sin wanda ke jagorantar tawagar kasar Sin a wajen shawarwarin, inda ya bayyana cewa, tawagar kasar Amurka za ta tashi zuwa kasar Sin don gudanar da shawarwari a sabon zagaye a tsakiyar watan Faburairun, kuma cewa ya yi yana fatan ganawa da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping tun da wuri, al'amuran da suka shaida cewa, Amurka na fatan cimma sakamako a shawarwarin da aka yi. A shawarwarin da aka gudanar a wannan karo, sassan biyu sun bayyana abubuwan da ke damunsu, haka kuma su yi kokarin neman cimma daidaito a kai, matakin kuma da ya kai ga cimma wannan muhimmin sakamako.

Sakamakon da sassan biyu suka samu ya nuna hikimar gwamnatin kasar Sin a fannin siyasa da basirarta a fannin daidaita matsala. Tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje kafin shekaru 40 da suka gabata, ta taba daidaita matsaloli daban daban saboda ta fahimci huldar dake tsakanin "rikici" da "dama". Misali tun farkon da ta shiga kungiyar cinikayyar duniya a shekarar 2001, kamfanonin kasar Sin sun fara fuskantar gogayyar dake tsakanin kasa da kasa kai tsaye, a sanadin haka, yawancinsu sun fama da manyan matsaloli, har sun ji tsoro matuka. Amma yanzu shekaru 17 sun wuce, kamfanonin kasar sun samu babban ci gaba ta hanyar kyautata tsarin sana'o'insu, karfin gogayyarsu a fadin duniya shi ma ya daga a bayyane.

A don haka yadda ake daidaita matsalar tattalin arziki da cinikayyar dake tsakaninta da kasar ta Amurka, shi ne sabuwar jarrabawar da take fuskanta a sabon zamanin da ake ciki yanzu, wato ya dace a sauya "rikici" zuwa "dama". Bisa matsaya guda da aka cimma yayin tattaunawar tattalin arziki da cinikayya da manyan jami'an kasashen biyu suka yi, kasar Sin za ta kara shigo da kayayyakin aikin gona da kayayyakin makamashi da kayayyakin masana'antu da kayayyakin samar da hidima daga kasar Amurka, hakan zai kara samar da damammaki ga masu sayayya na kasar Sin, shi ma zai kyautata tsarin sana'o'in kasar ta Sin. Game da rokon da Amurka ta gabatar, wai ya kamata kasar Sin ta yi gyaren fuska kan tsarin tattalin arzikinta, mun yi nazari sosai, sa'an nan mun lura cewa, ban da wasu bukatu wadanda ke shafar babbar moriyar kasa da tunanin al'ummar kasar da kuma tsaron kasar, ko shakka babu ba zai yiyu ba mu amince da su, saura wasu kuwa sun dace da muradunmu na yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. Misali Amurka ta bukaci kasar Sin da ta kara karfafa matakan kare ikon mallakar fasaha tare kuma da kara habaka kasuwarta, kasar Sin ta riga ta rubuta ka'idar kara cin tara ga masu aikata laifi a cikin daftarin dokar kare ikon mallakar fasaha, haka kuma an riga an aiwatar da tsarin tafiyar da jarin waje bisa doka, kana sake duba dokar zuba jari ta 'yan kasuwan kasashen waje ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali matuka kan matsayin daidai wa daida na jarin gida da jarin waje da kuma ka'idar adalci dake tsakaninsu yayin yin takara.

Ko kasancewar rigingimu a tsakanin kasashen Sin da Amurka ta fuskar tattalin arziki da cinikayya ko a'a, babu shakka kasar Sin za ta kara bude kofa ga waje yin yin kwaskwarima a gida. A waje daya kuma, ya kamata a lura da cewa, wasu bukatun da bangaren Amurka ya gabatar sun dace da hanyoyin da Sin ke bi wajen bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida. Don haka kasar Sin ta mayar masa martani cikin yakini. Lamarin kuwa da zai sa kaimi ga kyautata ingancin bunkasuwar tattalin arziki. Irin wannan tunani ba ma kawai zai taimaka wa kasar Sin wajen tinkarar sauye-sauyen yanayin duniya a halin yanzu yadda ya kamata ba, har ma zai taimaka wajen samun sabuwar hanyar warware matsalar da ke tsakanin sassan biyu yayin da suke yin shawarwari.

Ko shakka babu, sakamakon rigingimu a tsakanin kasashen Sin da Amurka ta fuskar tattalin arziki da cinikayya da dai sauran dalilai, yanzu tattalin arzikin kasar Sin ta samu dan tabarbarewa, amma har yanzu akwai babbar damar da ke gabanta wajen kara samun ci gaba. Sin na dora muhimmanci kan ayyukan kyautata tsarin tattalin arziki, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da kara bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida, da samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da ma sa hannu a cikin aikin gyara tsarin gudanar da harkokin tattalin arzikin duniya. Duk wadannan sun ba Sin imani wajen tinkarar ringigimun tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka da ma warware matsalar yadda ya kamata.

A wajen shawarwarin da aka yi a wannan karo, kasar Amurka ta ce za ta mayar da martani cikin tsanake bisa damuwar da kasar Sin ta nuna. A sa'i daya kuma, bangarorin 2 sun yarda da cewa kafa wani tsari don aiwatar da matakan da aka tabbatar da su na da muhimmanci sosai. Da ma Sinawa su kan ce "kaso 10 na wani aiki ya shafi tsara shiri, yayin da kaso 90 suka shafi aiwatarwa". Wannan maganar ta nuna yadda Sinawa suke dora muhimmanci kan cika alkawari, da neman samun sakamako.

Bayan da kasar Sin ta shiga kungiyar ciniki ta duniya WTO, ta riga ta cika alkawuran da ta yi masu alaka da cinikin kayayyaki, da cinikin hidima, gami da aikin kare ikon mallakar ilimi. Lamarin da ya sa tsohon babban sakataren kungiyar WTO Pascal Lamy ya baiwa kasar yabo sosai.

Yayin da ake neman daidaita takkadamar ciniki da tattalin arziki da ake samu tsakanin Sin da Amurka, kasar Sin ta nuna cikakken sahihanci a kokarinta na neman musayar ra'ayi da kasar Amurka, haka kuma ta cika dukkan alkawuran da ta dauka. Sai dai bangaren Amurka na ta kwan gaba kwan baya, abin da ya janyo damuwa sosai. Don aiwatar da ra'ayi daya da shugabannin Sin da Amurka suka samu, dole ne kasashen 2 su mutunta juna, gami da kokarin cika alkawari. A wajen shawarwari na wannan karo, an cimma matsaya dangane da tsarin da za a kafa wajen aiwatar da matakan da aka tabbatar da su, hakan zai taimakawa ba da tabbaci ga samun biyan bukatunsu na cika alkawarin da aka dauka.

A hakika dai, babban ci gaban da kasashen biyu suka samu a fannin mu'amalar ciniki a wannan karo, zai ba da taimako ga kasar Amurka wajen warware matsalar da take fuskanta. Tun daga tsakiyar watan Oktoba na shekarar 2018, kasuwar hannayen jari na kasar Amurka ta yi ta karuwa da raguwa na bai dace ba, har ma'aunin PMI ya ragu zuwa adadin da ba a taba gani ba a watan Disamba na shekarar 2018. Kwanan baya, ofishin kula da kasafin kudi na majalisar dokokin kasar Amurka ya fidda labari cewa, cikin shekaru 10 masu zuwa, adadin karuwar ma'aunin tattalin arizki na GDP na kasar Amurka zai ragu da 0.1% cikin kowace shekara, idan kasar ta ci gaba da tsarin harajin kwastan da take amfani da shi a halin yanzu. Kamar yadda a kan ce, a wurin dake da kalubaloli, mu kan gamu da damammaki, wani lokaci, kalubale ya iya canja zuwa dama mai kyau. Idan kasashen Sin da Amurka su ci gaba da mu'amalar dake tsakaninsu, za su iya samun sabbin damammaki na cimma moriyar juna, a yayin da suke aiwatar da ra'ayin daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma. (Masu Fassarawa: Lubabatu Lei, Jamila Zhou, Kande Gao, Bello Wang, Maryma Yang, ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China