in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya liyafar murnar sabuwar shekarar Sinawa ga kafofin watsa labarai a ofishin jakadancin Sin a Najeriya
2019-02-01 13:25:39 cri

Jiya Alhamis ofishin jakadancin kasar Sin dake tarayyar Najeriya ya shirya liyafar munar zuwan sabuwar shekarar Sinawa musamman domin kafofin watsa labarai a cibiyar yayata al'adun kasar Sin dake Abuja, fadar mulkin Najeirya, inda jadakan kasar Sin dake Najeriya Zhou Pingjian ya yi cikakken bayani kan ci gaban da kasashen biyu wato Sin da Najeriya suka samu yayin da suke aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya.

Yayin liyafar da ofishin jakadancin kasar Sin dake tarayyar Najeriya ya shiryawa kafofin watsa labarai, jakada Zhou Pingjian ya yi bayani kan ci gaban da kasashen biyu wato Sin da Najeriya suka samu yayin da suke aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, ga masu jagorancin muhimman kafofin watsa labarai da shahararrun kwararru da masana da editoci da 'yan jarida na kasar ta Najeriya, da farko, ya yi cikakken bayani kan babban bikin bazarar Sinawa dake tafe gare su, kana ya kara da cewa, za a cika shekaru 48 da kulla huldar diplomasiyya dake tsakanin Sin da Najeriya a ranar 10 ga watan Fabrairun da muke ciki, an lura cewa, hadin gwiwa mai inganci daga dukkan fannoni dake tsakanin Sin da Najeriya wato manyan kasashe masu tasowa wadanda ke kawo babban tasiri ga yanayin da kasashen duniya ke ciki, zai kawo babbar moriya ga al'ummomin kasashen biyu, haka kuma zai kasance abin koyi ga sauran kasashen Afirka yayin da suke gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu da kasar Sin.

Jakadan ya ce, a cikin shekarun baya bayan nan, fahimtar juna a fannin siyasa dake tsakanin kasashen biyu yana kara karfafuwa sannu a hankali, hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu shi ma ya samu babban sakamako, ko shakka babu makomar hadin gwiwar tana da haske matuka, ana iya cewa, huldar dake tsakaninsu ta samu ci gaba yadda ya kamata.

A watan Satumban bara, shugaban tarayyar Najeriya Mohammadu Buhari ya halarci taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a birnin Beijing na kasar Sin, inda ya cimma matsaya guda da shugaban kasar Sin Xi Jinping kan batun game da yadda zasu kara zurfafa huldar dake tsakanin kasashensu, Sin da Najeriya su ma sun daddale yarjejeniyar fahimtar juna kan hadin gwiwa wajen aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya.

Jakada Zhou ya yi nuni da cewa, hadin gwiwa tsakanin Sin da Najeriya ya samu babban sakamako a shekarar 2018, misali layin dogon da kamfanin kasar Sin ya gina a Abuja ya fara aiki, tashar ruwan Harcourt da sabon filin saukar jiragen saman Abuja su ma sun fara aiki, kana an fara gina hanyar mota ta Abuja-Keffi-Lafia-Makurdi, ban da haka kuma ana ci gaba da gudanar da aikin gina layin dogo tsakanin Lagos da Ibadan da tashar samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da karfin ruwa ta Zungeru da tashar ruwa mai zurfi ta Lekki da sauransu, duk wadannan sun alamanta cewa, huldar dake tsakanin kasashen biyu ta shiga wani sabon mataki a tarihi.

Jakadan ya kara da cewa, bana shekara ta farko ce da Najeriya ta shiga shawarar ziri daya da hanya daya a hukumance, duk da cewa, kasar Sin ta gabatar da shawarar, amma tana shafar daukacin kasashen duniya, haka kuma zata amfanawa daukacin al'ummomin kasashen duniya baki daya. A don haka kasar Sin tana nacewa ga manufar bude kofa ga kasashen waje, tare kuma da sa kaimi kan hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya, ta yadda zata samar da wani sabon dandalin hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa, domin cimma burin samun ci gaba tare a fadin duniya.

Zhou Pingjian ya ce, za a gudanar da dandalin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar ziri daya da hanya daya karo na 2 a birnin Beijing a watan Aflilun bana, tabbas ne lamarin zai ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Najeriya gaba yadda ya kamata.

A karshe dai jakadan ya bayyana cewa, bana cika shekaru 70 ne da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, kasar Sin zata ci gaba da yin kokari tare da Najeriya domin daga matsayin huldar dake tsakaninsu, tare kuma da kawo alheri ga al'ummomin kasashen biyu.

Yayin liyafar, jami'in yayata al'adun kasar Sin dake ofishin jakadancin kasar Sin a Najeriya kuma darektan cibiyar yayata al'adun kasar Sin dake kasar Li Xuda ya yi bayani ga mahalarta liyafar kan bikin murnar bikin bazarar kasar Sin karo na 3 da za a bude a ranar 2 ga wata wato gobe ke nan.

Hakazalika, masu jagorancin muhimman kafofin watsa labarai da shahararrun kwararru da masana da editoci da 'yan jarida na kasar ta Najeriya wadanda suka halarci liyafar su ma sun kalli nune-nunen da aka shirya kan sakamakon da kasar Sin ta samu a cikin shekaru 40 da suka gabata wato tun bayan da aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China