in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci nahiyar Afrika ta samar da dabarar rage rashin aikin yi
2019-02-01 11:39:15 cri
Hukumar kwadago ta MDD, ta bukaci gwamnatocin Afrika da kungiyoyin kwadago su hada hannu wajen samar da dabarar kara yawan ayyukan yi.

Susana Puerto, kwararriya kan harkar samarwa matasa aikin yi ta kungiyar kwadago ta duniya ILO, ta shaidawa wani taro a Nairobin Kenya cewa, galibin matasan Afrika na ayyuakan da ba su da tsarin gudanarwa. A don haka suke kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su hada hannu wajen tabbatar da matasan nahiyar sun samu ayyukan yi da suka dace.

Duk da yadda aka dauki lamarin da girma, matakin rashin aikin yi a yankin kudu da hamadar Sahara ya tsaya ne kan kwatankwaci kaso 12 cikin 100.

Ta kara da cewa matakin aikin yi a Afrika na sama sosai, saboda tilas ne matasa su samu abun yi, a don haka ne kuma suke yin kowanne irin aiki dake akwai.

A nasa bangaren, Daraktan Zartarwa na cibiyar bincike kan harkokin tattalin arzikin Afrika, Njuguna Ndung'u, cewa ya yi, har yanzu rashin aikin yi na daya daga cikin kalubalen gaggawa dake fuskantar masu tsara manufofi a Afrika. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China