in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"Kyautata tsarin sana'o'i" yayin da kasar Sin ke zuba jari a ketare ya zama sabon abun dake jawo hankulan mutane
2019-01-31 22:05:12 cri

A lokacin da karin kamfanonin kasar Sin suke kafa sassansu a ketare, jari nawa kasar Sin ta zuba a ketare? Masana'antu nawa da kamfanonin kasar Sin suka zuba jari suka kafa a ketare kai tsaye? Kana ma mene ne sabon jigo da kuma sabon abu dake da nasaba da jarin kasar Sin a ketare? Dukkansu sun zama batutuwan dake jawo hankulan gida da na waje. A cikin "rahoto game da jarin da kasar Sin ta zuba a ketare na shekarar 2018", an ba da amsa kamar yadda ake fata.

A cikin rahoton, an waiwayi yadda kamfanonin kasar Sin suka zuba jari kai tsaye a ketare a shekarar 2017, sannan an nazarci rawa da tasirin da jarin kasar Sin yake takawa a duniya. Bugu da kari, an yi la'akari da yadda kamfanonin kasar Sin suke samun bunkasa, da kuma makomar da kasar Sin take da ita a nan gaba a fannin zuba jarinta a ketare kai tsaye. Bisa rahoton da aka bayar, an ce, ya zuwa shekarar 2017, yawan jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba a ketare ya kai dalar Amurka triliyan 1.8, wato ya karu da kaso 33.3% bisa na shekarar 2016, sannan wannan adadi ya kuma kai kaso 5.9%, bisa jarin da dukkan kamfanonin kasa da kasa suka zuba a ketare.

Ko shakka babu, yanzu kasar Sin babbar kasa ce wajen zuba jari a ketare. Yawan jari da tasirinta suna ta samun karuwa. A yayin da wasu kasashen suke kokarin daukar matakan hana yin cinikayya tsakanin kasa da kasa cikin 'yanci, ba a san ina makomar rikicin cinikayya da ake yi tsakanin kasashen Sin da Amurka, har ma wasu kasashe masu arziki sun kara sa ido kan jarin waje ba, "kyautata tsarin sana'o'i" da yin rigakafin aukuwar hadari, sun zama muhimman batutuwan da kasar Sin take yi a yayin da take zuba jari a ketare.

Bayan da kasar Sin ta kaddamar da "rahoto game da yadda kasar Sin take zuba jari a ketare" cikin shekaru 10 da suka gabata, a bayyane take an bayyana cewa, kasar Sin na tabbatar da aiwatar da manufofinta na zuba jari a ketare sannu a hankali. Bisa wannan sabon rahoton da aka fitar a kwanan baya, an ce, sana'o'in da kasar Sin take zubawa a ketare sun samu kyautatuwa sosai. Da farko dai, kasar Sin ta ci nasarar hana a kara zuba jari a fannonin samar da gidaje, da otel-otel, da gidajen sinima, da sana'ar jin nishadi, da kuma kulob-kulob din na wasannin motsa jiki, domin kokarin yin rigakafin aukuwar hadarin hada-hadar kudi. Amma yanzu kasar Sin tana karfafa gwiwar kamfanoninta da su zuba jari a ketare a fannonin masana'antu, da sana'o'in gargajiya, da kuma wasu sana'o'in dake da nasaba da sabbin fasahohin zamani, har ma a fannin aikin gona.

Wani fanni na daban ya shafi yadda aka kyautata tsarin da ya shafi yankuna, wato kasar Sin ta canza tsarin da take bi wajen zuba jari a ketare, da yankuna daban daban. Yanzu kasar Sin ta fi zuba jarinta ga kasashe makwabta, musamman kasashen dake kudu maso gabashin Asiya, da kungiyar kasashen tsohuwar tarayyar Soviet.

A sa'i daya, kasar Sin ta kara zuba jari ga kasashen Turai da Amurka, wadanda ke da ci gaban tattalin arziki. Hakan ya nuna yadda kamfanonin kasar Sin suke tsananin bukatar fasahohi masu ci gaba, da dabarun kula da kamfani, da sanannun lambobin kasuwanci, da dai makamantansu, a kokarin kasar na kyautata tsakanin tattalin arzikinta.

Ban da wannan kuma, kasashe da yankuna da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" ta shafa, sun zama inda aka fi janyo jari daga kasar ta Sin. Tsakanin shekarar 2013 zuwa ta 2017, kasar Sin ta zuba ma kasashe masu alaka da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" kudin da ya kai dalar Amurka biliyan 82. Hakika a shekarar 2017 kawai, kudin da kasar Sin ta zuba ma wadannan kasashe ya kai dala biliyan 20, adadin da ya karu da fiye da kaso 3 idan an kwatanta da na shekarar 2016. Haka kuma, ana ganin yadda zuba jarin ya shafi karin sana'o'i, inda ana ta kokarin sayen wasu kamfanoni.

Duk a rana Talata, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta gabatar da "Takardar bayanin jagorar aikin zuba jari a ketare ta shekarar 2018". Cikin takardar an bayyana yanayin da kasashen da ake sha'awar zuba musu jari ke ciki, wanda ya shafi tattalin arziki, manufofin gwamnati, da dokoki, da damammaki gami da haduran da ake fuskantar. Ta wannan hanya aka baiwa kamfanonin kasar Sin dimbin bayanan da suke bukata, domin gudanar da aikin su na zuba jari a kasashen waje, sa'an nan an ba su shawara kan matakan da za su iya dauka don daidaita matsalolin da ka iya gamuwa da su, don taimaka musu gudanar da harkokinsu yadda ake bukata a kasashe daban daban. (Masu Fassarawa: Sanusi Chen, Bello Wang, ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China