Yayin ganawar, shugaba Xi ya ce kasar Sin tana dora cikakken muhimmanci kan aikin karbar bakuncin gasar Olympics ta lokacin sanyi ta shekarar 2022 a birnin Beijing. A cewar shugaban, daukacin jama'ar kasar Sin za su yi kokarinsu, don shirya wata gasar Olympics irin ta kare muhalli, wadda za ta amfani kowa, ta bude kofa domin kowa ya halarta, wadda kuma za ta zama mai tsabta, wato ba tare da aikata zamba a cikin ta ba.
A nasa bangaren, Tomas Bach ya ce, yana da imanin cewa, kasar Sin za ta iya karbar bakuncin gasar Olympics mai kayatarwa. (Bello Wang)