Na farko, kasashen sun yi alkawarin daukar nauyin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya. Na biyu, sun sha alkawashin kiyaye tsarin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya. Na uku, sun ce za su ci gaba da musayar ra'ayoyi, musamman ma ta hanyar taron da za su rika shiryawa tsakaninsu.
A cewar Geng Shuang, wannan sakamako ne da aka samu, wanda zai karfafawa gamayyar kasa da kasa gwiwarsu kan yanayin tsaro a duniya. (Bello Wang)