in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron manema labaru game da bikin kade-kade da raye-raye na murnar shiga sabuwar shekara na kasar Sin
2019-01-31 19:04:23 cri

A yayin da ake jiran ganin bikin kade-kade da raye-raye na murnar shiga sabuwar shekara da za a gabatar da shi a ranar 4 ga watan Fabrairu, wato jajibirin bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, kan telabijin, a yau Alhamis, babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ya kira taron manema labaru, don yin bayani kan fasahohin al'adun da za a nuna, gami da sabbin fasahohi na zamani da za a yi amfani da su wajen bikin.

Jiang Wenbo, wani jami'in kamfanin CMG ya bayyana cewa, za a yi amfani da fasahohi mafi ci gaba, da na'urori mafi inganci wajen tsara bikin na murnar sabuwar shekara. Sa'an nan fasahohin da za a yi amfani da su wajen nuna bikin sun hada da 4K, 5G, VR, AR, da AI, da dai makamantansu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China