in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda shugaba Xi Jingping yake kula da 'yan kabilu daban daban na kasar Sin
2019-02-10 16:49:37 cri

"Ya kamata al'ummomi daban daban su zama tsintsiya madaurinki daya", "A kokarin neman walwala, bai kamata a bar wata kabila a baya ba"...Wadannan jimlolin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi, sun nuna burinsa na samun hadin kan al'ummomin kasar Sin, da ci gaban zaman rayuwarsu baki daya. Kasar Sin kasa ce da yawan kabilunta ya kai 56, kana wasu daga cikinsu sun dade suna zama a wasu yankuna masu nisa, inda ba a samu ci gaban tattalin arziki sosai ba. Ta yaya za a tabbatar da jin dadin zaman rayuwar al'ummomi daban daban? Wannan tambaya ce da Xi Jinping, shugaban kasar Sin ke kula da ita a ko da yaushe.

"Yau ina farin ciki matuka, domin kun zo daga wani wuri mai nisa."

A shekarar 2015, yayin rangadinsa na farko a wani wuri dake waje da birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi ga wasu 'yan kabilar Dulong ta lardin Yunnan na kasar Sin. 'Yan kabilar Dulong suna zama a wani kauyen dake cikin duwatsun, haka kuma, wuyar zirga-zirga a wurin ta sa mutanen wurin shan wahala sosai. A karshen shekarar 2014, wasu jama'ar wurin sun rubuta wasika ga shugaba Xi Jinping, don ba shi wani labari mai dadi, cewar za su fara yin amfani da wani ramin da aka haka, inda wata hanyar mota za ta ratsa shi. Daga bisani, lokacin da Xi ya yi rangadi a lardin Yunnan, ya gayyaci wasu 'yan kabilar Dulong, wadanda suka rubuta masa wasika, don su je wurin da ya sauka su yi hira. A lokacin ganawarsu, shugaba Xi ya ce,

"Duk da cewa yawan al'ummar Dulong 6900 ne kawai, wannan kabilar tana da matsayin iri daya da na sauran kabilun kasar Sin 55. Nauyin da ya rataya a wuyanmu shi ne farfado da al'umma, da neman cika burin da kasarmu ta saka gaba. Yayin da ake wannan aiki kar a bar wata kabila a baya, ya kamata a tabbatar da ganin dukkansu sun samu walwala."

A wani waje na daban kuma, jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, babbar jiha ce ta kasar Sin, wadda fadinta ya kai kimanin kashi 1 cikin kashi 6 na fadin kasar. A wannan jiha, ana samun kabilu daban daban, da suka hada da Han, da Uygur, da Khazak, da dai sauransu, wadanda baki daya yawansu ya kai 47. Saboda haka, kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arzikin jihar suna janyo hankalin shugaba Xi Jinping sosai. A watan Fabrairun shekarar 2014, yayin da ya yi ragadinsa na farko a jihar Xinjiang tun bayan da aka kammala taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18, Xi Jinping ya tafi Kashgar dake kudancin jihar. A gidan wani dan kabilar Uygur mai suna Abdulkimu Rozi, Xi Jinping ya duba dakinsa na karbar baki, da dakin girki, da gidan tumaki, da lambun 'ya'yan itatuwa, gami da injunan noma, ya kuma yi tambaya kan yanayin zaman rayuwarsu.

"Na zo nan don duba ko manufar gwamnatin tsakiya ta kyautatawa jama'a ta yi amfani, ko jama'a sun yarda da manufar."

Haka zalika, shugaba Xi Jinping yana mai da hankali kan aikin tabbatar da hadin kan al'ummomin dake jihar Xinjiang matuka. Ya jaddada cewa,

"Hadin kan al'ummomi tushe ne ga ci gaban jihar Xinjiang, kuma dukkan jama'ar kasar Sin fiye da miliyan 1300 sun yarda da haka. Ya kamata mu yi kokarin kare hadin kan al'ummomi daidai kamar yadda ake kokarin kare idanu. Ya kamata mu dora cikakken muhimmanci kan hadin kan al'umma, daidai kamar yadda ake kula da rai."

Ban da haka, a jihar Ningxia ta kasar Sin ana samun wani yanki mai talauci. Shugaba Xi Jinping ya taba ziyartar wurin, ya kuma tuna da cewa,

"Na zo nan a shekarar 1997, a lokacin yadda ake fama da tsananin talauci ya ta da min hankali sosai. Don haka na yi kokarin kulla hulda tsakanin yankunan Ningxia da na Fujian, don kaurar da mutane daga yanki maras muhalli mai kyau zuwa wani wurin da zai baiwa musu muhallin zaman rayuwa."

A lokacin da Xi Jinping yana rike da mukamin mataimakin sakataren reshen kwamitin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin a lardin Fujian, ya ba da shawarar kafa kauyen Minning a lardin Fujian don karbar mutanen da aka kaurar daga yankuna masu talauci dake jihar Ningxia. Bayan wasu shekaru 20, kauyen Minning mai jama'a 8000 ya zama wata gunduma mai mutane dubu 60, inda mazauna wurin ke jin dadin zaman rayuwarsu bayan an biya musu bukatunsu a dukkan fannonin kamar samun ruwa, da zirga-zirga, gami da wutar lantarki.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China