in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutum Miliyan 10 Ke Shan Wiwi A Nijeriya
2019-01-31 15:47:29 cri
Bisa labarin da muka samu daga shafin "Leadership A Yau": A ranar Talata ne Hukumar kididdiga ta kasa 'National Bureau of Statistics' ta gabatar da rahoto a kan yadda ake amfami da miyagin kwayoyi a kasar nan, inda ta ce, kashi 14.4 na 'yan Nijeriya ke amfani da miyagin kwayoyi a halin yanzu.

Hukumar ta gabatar da rahoton ne a shafinta na intanet, inda ta kara da cewa, kashi 14.4 ke zukan miyagin kwayoyi abin dake nuna cewa, kusan mutum Miliyan 14.3 ke na daga cikin 'yan Nijeriya ke mu'amala da kwayoyin.

Hukumar ya kuma bayyana cewa, mu'amala da miyagun kwayoyi ya yi matukar karuwa in aka kwatanta da yadda lamarin yake a shekarar 2016, inda kashi 5.6 ne ke shan miyagin kwayoyin.

Sun kuma kara cewa, a Nijeriya, daya daga cikin mutum bakwai na daga shekaru 15 zuwa 64 yana amfani da wani nau'in taba sigari ko kuma barasa kai tsaye.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, daga ciki duk mutum 4 masu amfani da miyagun kwayoyi a Nijeriya za ka samu akwai mace a ciki.

Shan kwayoyi ya fara ne daga 'yan Nijeriya masu shekara 25 zuwa 39.

Hukumar NBS ta kuma bayyana cewa, an fi amfani a taba wiwi daga cikin miyagun kwayoyin da ake amfani da su, inda aka ruwaito cewa, mutum Miliyan 10.6 ke zukan taba wiwi a duk shekara fadin Nijeriya.

Rahoton ya kuma kara da cewa, "Zukan wiwi ya tashi daga kashi 7 a cikin dari a tsakain maza da kashi 18.8 yayin da kuma mata suka kai kashi 2.6, haka kuma wadanda suke amfani da kwayoyin a wajen neman magani sun kai kashi 3.3 a cikin mazaje yayin da kuma mata suka kai kashi 6, irin kwayoyin da ake amfani da su wajen magani sun hada da Tramadol."

Haka kuma rahoton ya kuma bayyana cewa, anfi amfani da miyagun kwayoyin a yankunan Kudancin kasar nan inda abin ya kai kashi tsakanin 13.8 zuwa kashi 22.4, inda aka hada da yadda lamarin yake a yankin Arewacin kasar nan na kashi 10 zuwa kashi 13.6.

Rahoton ya kuma kara da cewa, kashi 40 na masu amfani da kwayoyin sun nuna alamun bukatar taimakon magani da gagawa saboda alamun cutar hauka daya bayyana a kansu.

"Yawanci masu amfani a kwayoyi su kan samu mastala wajen samun tallafin magani, musamman ganin yadda magungunan kan kasance da tsadar gaske da kuma kyama da ake nuna mus ua yanwancin lokutta,"

Rahoton ya kuma kara da cewa, an fi samun matsalar samun magani ga masu mu'amala a kwayoyi daga jihohin Yobe da Imo da Bayelsa da Ribas da kuma Legas."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China