in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin samar da sadarwar talabijin a kauyukan Afirka
2019-01-31 14:49:28 cri





Shirin samar da sadarwar talabijin a kauyukan Afirka, wani mataki ne da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dauka ta fannin hadin gwiwar al'adu a matsayin Sin da kasashen Afirka a gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a shekarar 2015 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, matakin da ke da nufin samar da sadarwar talabijin na zamani na tauraron dan Adam a kauyuka sama da dubu 10 da ke fadin kasashen Afirka fiye da 30. Kasar Mozambique da ke kudancin nahiyar Afirka na daya daga cikin kasashen Afirka da shirin ya shafa, inda tun bayan da aka fara aiwatar da shirin, aka samar da sadarwar talabijin a kauyuka 500 da ke fadin kasar, wanda kuma ya amfanawa al'ummar kauyuka sama da dubu 50.

Marracuene, wani kauye ne da ke da tazarar kilomita 70 da ke arewacin birnin Maputo, babban birnin kasar, kuma Helton Wiliamo yana rayuwa ne cikin wannan kauye. Gidan Helton Wiliamo na daya daga cikin gidaje 20 da ke cikin kauyen, wadanda aka samar musu sadarwar talabijin. Kafin kaddamar da shirin, wasu shirye-shiryen kafofi biyu na gidan talabijin na kasar ne kawai yake iya samu, amma ga shi yanzu, yana iya kallon shirye-shiryen kafofi sama da 30, wadanda suke kara samar musu bayanai da kuma nishadantarwa. Helton Wiliamo ya ce,"Na taki sa'a sosai da aka samar mana sadarwar talabijin ta zamani, ga shi yanzu ina iya kallon shirye-shiryen talabijin masu inganci, ko da an yi ruwa da iska ma, ba a samun matsala. Ban da wannan, shirye-shiryen da muke iya kallo ma sun karu, misali akwai fina-finan wasan Kungfu da suke ba ni sha'awa, akwai kuma shirye-shirye na yara, duka muna samu."

Bisa ga shirin da ake aiwatarwa a kasar Mozambique, a kan zabi wasu gida 20 dake cikin kowane kauye, don kafa musu na'urorin karbar sadarwar talabijin na zamani ba tare da sun biya ko sisi ba. Sa'an nan, ta wadannan na'urorin da aka kafa ne ake samar da shirye-shiryen talabijin ta wasu kafofi 31, wadanda cikin wata na farko ake kallo ba tare da biyan kudi ba, daga wata na biyu kuma, dala uku ne kawai za a biya a kowane wata don kallon shirye-shiryen. Baya ga haka, ana kuma kafa na'urori a wasu sassa na taruwar al'umma da suka hada da asibiti da makaranta da cibiyoyin nishadantarwa, don samar musu shirye-shiryen talabijin a kyauta.

Makarantar firamare ta farko da ke kauyen Marracuene na daya daga cikin sassan taruwar jama'a da aka samar da sadarwar talabijin ta zamani. A watan Mayun shekarar 2018, aka gudanar da bikin kaddamar da shirin samar da sadarwar talabijin na zamani a kasar Mozambique a cikin makarantar, kuma shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Li Zhanshu wanda a wancan lokaci ke ziyara a kasar ya halarci bikin. A yayin bikin, Li Zhanshu ya ce, sadarwar talabijin na zamani da aka samar sun kasance tamkar ido da kunne, wadanda za su taimaka wa mazauna kauye wajen fahimtar halin da ake ciki a kasashe daban daban, don haka, lamarin na da ma'ana sosai.

Gabriel Mabjaia, shugaban makarantar ya ce, yanzu a kowane sati, makarantar ta kan tara dalibanta a wuri daya don su kalli shirye-shiryen talabijin. Ya ce,"Yadda ake samar mana sadarwar talabijin na zamani, abu ne mai kyau sosai, sabo da ta haka ne yara a makarantar za su iya kallon shirye-shiryen talabijin ta kafofi da dama, wadanda za su taimaka musu fahimtar abubuwan da ke faruwa a kasar Mozambique da ma sauran kasashen duniya. Domin biyan bukatun 'yan makarantar sama da 900, mun tsara shiri, kuma bisa ga shirin, 'yan makarantar su kan zo nan kallon shirye-shirye cikin rukunoni uku, sau uku a kowane mako. Shirye-shirye na yara da ma na ilmantarwa suke kallo, wadanda ban da nishadantarwa, za su kuma taimaka ga inganta ilmin da suka koya daga darussa."

Kamfanin Startimes shi yake daukar nauyin aiwatar da shirin nan na samar da sadarwar talabijin a kauyukan Afirka, kuma Mr. Yu Wenyu shi ne babban darektan sashen gudanarwa na reshen kamfanin da ke kasar Mozambique. Ya ce, a lokacin da ake aiwatar da shirin, an fuskanci matsaloli da dama da ba a tsinkaya ba. Misali, rashin ingancin hanyoyin zuwa kauyukan, musamman ma a lokacin damina, ya kan hana motocin injiniya shiga kauyuka. Sa'an nan, akasarin gidaje da ke cikin kauyukan da katako aka gina su, don haka ba su dace a kafa na'urorin karbar sadarwar talabijin a kai ba. Duk da haka, Yu Wenyu ya ce, kwalliya ta biya kudin sabulu, la'akari da yadda mazauna kauyen ke jin dadin shirin, ya ce,"Shirin ya samu karbuwa sosai a kasashen Afirka, kuma suna fatan za a kara samar musu wannan hidima. Don haka, ni ma ina fatan za a fadada shirin, don karin al'ummar kasashen Afirka za su jin dadin sadarwar talabijin na zamani."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China