in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in hukumar agajin MDD ya jaddada bukatar shigar da kayan tallafi Syria
2019-01-31 10:55:46 cri

Babban jami'in hukumar samar tallafin jin kai ta MDD Mark Lowcock, a ranar Laraba ya jaddada bukatar samun damar shiga kasar Syria don mika kayayyakin tallafi ga mutanen dake cikin halin bukata, musamman a yayin da ake fuskanta na matsanancin sanyi.

Lowcock, wakilin babban sakataren MDD mai kula da ayyukan jin kan al'umma, ya ce tawagar jami'an ba da agajin suna dakon samun ikon kai dauki ga mutane kimanin dubu 42 dake gararamba a yankin Rukban dake kan iyakar kasashen Syria da Jordan.

MDD tana ci gaba da yin bakin kokarinta, sai dai kasashen Rasha da Syria suna bayyana fargabar tsaro kan tawagar bayar da agajin da sanyan ido wajen rarraba kayan tallafin jin kai, in ji Lowcock

Tawagar ta kunshi manyan motoci 100 makare da kayayyakin tallafi, da suka hada da abinci, kayan maganin sanyi da na kiwon lafiya, da abubuwa masu gina jiki, da na amfanin gida da ruwan sha mai tsabta da kuma alluran rigakafi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China