Kasashe 5 masu wakilcin din din din a kwamitin sulhun MDD, wato Sin, Faransa, Rasha, Birtaniya da Amurka, sun gudanar da wani taro a ranar Laraba a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin domin tattauna batutuwa dake shafar makaman nukiliya, inda suka sha alwashin yin hadin gwiwa da juna don kiyaye yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.
Kasar Sin a shirye take a ko da yaushe wajen gina tsarin cimma daidaito da kawar da banbance banbance a tsakanin manyan kasashen biyar game da batun dabarun tsaro, da ba da gudunmowa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya, in ji Zhang Jun, shugaban tawagar wakilan kasar Sin, kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar, ya bayyana hakan a lokacin da yake tsokaci yayin kammala babban taron.
Kasashen biyar, wadanda ke amfani da makaman nukiliya bisa doka, sun fara shirya taro tun a shekarar 2009, da nufin ci gaba da tuntubar juna game da batutuwan da suka shafi kiyaye tsaron makaman nukiliya. Kasar Sin a halin yanzu ita ce mai sulhuntawa kan hadin gwiwar.(Ahmad Fagam)