in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
JKS ta bayyana matsalolin da aka gano a nazarin da aka yi na baya-bayan nan
2019-01-31 10:34:56 cri

Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta fitar da sakamakon zagaye na biyu, na nazarin ladaftarwa da kwamitin tsakiya na jam'iyyar na karo na 19 ya yi.

Sabon zageyen ya maida hankali ne kacokan kan rage fatara, wanda shi ne karo na farko da babban kwamitin ya mayar da hankali kan maudu'i guda yayin gudanar da irin wannan nazari.

Nazarin ya kunshi tawagogi da aka tura hukumomin jam'iyyar a larduna 13, galibi na yankunan tsakiya da yammacin kasar Sin, kamar Anhui da Chongqing da Tibet da Xinjiang da kuma wasu sassan gwamnatin tsakiya 11 dake da alaka da aikin rage radadin talauci da wasu cibiyoyin kudi 2, ciki har da ma'aikatar kula da al'umma da kuma bankin raya aikin gona na kasar sin, a tsakanin watan Oktoba da Nuwamban bara.

Kasar Sin ta shirya rage adadin matalauta a yankunan karkara da sama da miliyan 10 a 2018, a wani banagre na kawo karshen fatara ya zuwa shekarar 2020. Nazarin zai bada tabbaci game da nasarar da aka samu wajen yaki da talauci a kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China