in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara sabon zagaye na tattaunawar cinikayya tsakanin Sin da Amurka
2019-01-31 10:13:52 cri

Da safiyar ranar Laraba kasashen Sin da Amurka suka bude sabon zagayen muhimmin taron tattaunawa da nufin lalibo bakin zaren warware sabanin ciniki da tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu.

Tattaunawar, wacce za'a shafe wuni biyu, wani muhimmin mataki ne na aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Donald Trump a lokacin wata ganawar da suka yi yayin wata liyafar cin abinci a birnin Buenos Aires, na kasar Argentina, a ranar 1 ga watan Disamban bara.

Shugabannin kasashen biyu sun amince a wancan lokacin cewa, bangarorin biyu za su yi kokarin cimma matsaya guda kan yarjejeniyar amfanawa juna da kuma cin moriyar juna cikin kwanaki 90, da nufin kawo karshen yakin cinikin da ya kaure tsakaninsu, wanda ya haifar da sakawa juna matsanancin haraji kan kayayyakin da suke shigi da fici a tsakanin bangarorin biyu.

An fara tattaunawar baya bayan nan ne da misalin karfe 9 na safe, agogon Washington, a babban ofishin Eisenhower, dake fadar White House, bayan wani takaitaccen ganawa da manema labarai da suka gudanar.

Tawagar wakilan kasar Sin, wanda mataimakin firaiministan kasar Sin Liu He, ya jagoranta, ta kunshi wasu manyan jami'an sashen tattalin arzikin kasar Sin, yayin da wakilin ma'aikatar cinikin Amurka Robert Lighthizer ya jagoranci tawagar wakilan kasar Amurka, wanda ya hada da sakataren kudin Amurkan Steven Mnuchin.

Fadar White House ta ce, Amurka tana maraba da wakilan bangaren Sin, wadanda suka isa birnin Washington tun a ranar Litinin, kuma an tsara Mr. Trump zai gana da Liu a yau Alhamis.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China